Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Habaka Da Kashi 22% A 2025 Bisa Gagarumar Gudunmawar Bangaren Cartoon

[ad_1]

Kasuwar fina-finai ta kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba a shekarar 2025, inda yawan tikitin kallon sinima da aka sayar a cikin shekarar ya karu da kusan kashi 22 cikin dari, zuwa kimanin yuan biliyan 51.83, kwatankwacin dala biliyan 7.37, sakamakon bunkasar da aka samu daga bangaren fina-finan hotunan zane (cartoon) da ba a taba ganin irinta ba, wanda daga nan ne aka samu kusan rabin jimillar kudaden, kamar yadda bayanan da hukumar fina-finai ta kasar Sin ta fitar a yau Alhamis suka bayyana.

Wannan gagarumin ci gaba, wanda ya biyo bayan jimillar Yuan biliyan 42.5 da aka samu a shekarar 2024, ya samu ne daga jerin fina-finai guda biyu masu ban mamaki, na farko shi ne fim din da aka shirya a cikin gida na “Ne Zha 2” wanda ya bude kofar samun ciniki a farkon shekarar, yayin da fim din “Zootopia 2” na Disney kuma ya habaka kasuwar a karshen shekarar. Duka su biyun, sun mayar da shekarar ta 2025 zuwa abin da masu sharhi kan masana’antar fina-finan suka kira da “shekarar tambarin cartoon,” tare da kalubalantar irin labarun da aka saba bayarwa a kasuwar fina-finan, kana suka jaddada cewa ba tare da la’akari da mene ne asalin gaskiyar labari ba, har yanzu tsara bayar da labari cikin inganci shi ne a kan gaba.

Bayan bangaren fina-finan zane-zanen na cartoon, akwai wasu sassa na fina-finan da suka samu tagomashi. Fina-finan yaki kamar na “Dead to Rights” da “Evil Unbound,” wadanda suka sami sama da yuan biliyan 3 da yuan biliyan 1.94 bi-da-bi, sun sami nasara ta hanyar amfani da mahangar kusanci da dan Adamtaka maimakon bayar da manyan labarai kawai. Masu sharhi sun kuma yi nuni da irin mabambantan abubuwan da ake samu a kasuwar fina-finai ta Sin, inda shirye-shiryen bidiyo, fina-finan fasaha daga bukukuwan fina-finan kasa da kasa da kuma wasu da aka shigo da su daga Turai, duk suka samu karbuwa a wurin wasu masu kallo. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *