An Sallami Anthony Joshua Daga Asibiti Bayan Hatsarin Mota

[ad_1]

An sallami shahararren ɗan damben Boksin ɗan asalin Nijeriya Anthony Joshua daga asibiti, kwanaki kaɗan bayan wani mummunan hatsarin mota da ya yi sanadiyar mutuwar abokansa biyu.

Tsohon zakaran duniyar ya murmure daga jinyar da yake yi, amma ya bayyana rashin ma tta ɗkusantansa a matsayin babban abi nda ke damunsa a yanzu.

  • ‘Yan Bindiga Sun Rage Kuɗin Fansar Matafiya 28 Da Suka Sace A Filato zuwa N30m
  • Jawabin Shugaba Xi Jinping Na Kasar Sin Na Taya Murnar Sabuwar Shekara Ta 2026

Joshua mai shekaru 36 fasinja ne a cikin wata mota kirar Lexus SUV wacce ta yi karo da wata babbar mota a kan babbar hanyar Ogun, kusa da Legas, a ranar Litinin.

Mutane biyu da suka mutu abokan Joshua ne kuma membobin tawagar dambensa, Sina Ghami da Latif “Latz” Ayodele.

Bayan barin asibiti a ranar Laraba, ɗan Birtaniyar ya ziyarci inda aka ajiye gawarwakinsu yayin da ake shirye-shiryen jana’izarsu.

Ghami shi ne mai kula da wasanni da motsa jiki a wajen Joshua na tsawon lokaci inda ya yi aiki tare da shi fiye da shekaru 10.

Da yake magana da BBC a ranar Laraba, mai magana da yawun ‘yansandan jihar Ogun Oluseyi Babaseyi ya ce “har yanzu ana ci gaba da bincike dangane da yadda al’amarin mai ya faru”.

Hukumar Kula da Dokokin Ababen Hawa (TRACE) a Jihar Ogun, inda hatsarin ya faru, ta ce binciken farko ya nuna cewa tayar motar ce ta fashe kafin ta tunkari babbar motar dakon kaya dake gefen hanya.

Joshua, wanda aka haifa a Watford amma asalin iyayensa ‘yan Nijeriya, ya zo domin hutun ƙarshen shekara bayan nasarar da ya samu a kan Jake Paul a Miami a ranar 19 ga watan Disamba, 2025.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *