Kotu ta sami Nnamdi Kanu da laifukan ta’addanci

[ad_1]



Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sami jagoran haramtacciyar ƙungiyar neman kafa kasar Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu, da laifukan ta’addanci da aka zarge shi da aikatawa.

Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, Mai Shari’a James Omotosho, ya amince da batutuwa uku da aka gabatar a shari’ar, inda ya yanke hukunci a kan su daga bangaren masu gabatar da ƙara.

Alkalin ya ce barazanar tashin hankali da Kanu ya yi a cikin jawabansa ta haifar da tsoro da damuwa a zukatan jama’a a yankin Kudu maso Gabas.

Justice Omotosho ya ƙara da cewa bisa hujjojin da masu gabatar da ƙara suka bayar, an tabbatar da abubuwan da suka hada da ta’addanci a cikin shaidun da aka gabatar a kan shi ta hanyar niyya da halayensa.

Alkalin ya lura cewa Kanu ya ki yak are kansa, yana mai cewa ya “gaza kuma da gangan ya ƙi bayar da wata hujja da za ta wanke shi” daga tuhumar da aka yi masa.

A halin yanzu dai kotun na ci gaba da yanke hukunci kan tuhumar ta’addanci da aka gabatar a kan Kanu.

Muna tafe da karin bayani…


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *