Matasa 16 Masu Shirin Fara NYSC Sun Rasu A Mummunan Hatsarin Mota

[ad_1]


Aƙalla matasa 16 ne daga cikin waɗanda suka kammala karatu a jami’ar ilimi ta Adeyemi (AFUED), dake jihar Ondo suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota mai muni yayin da suke kan hanyar zuwa sansanin horaswa na NYSC da ke jihar Gombe. Lamarin ya faru ne a safiyar Litinin, inda rahotanni suka tabbatar cewa mutum biyu kacal suka tsira, amma suna cikin mummunan yanayi a asibiti.

Shaidun gani da ido yayin hatsarin sun bayyana cewa motar haya ƙirar bas mai kujeru 18 ce ta yi taho-mu-gama a hatsarin, wanda ya janyo lalacewar motocin  tare da haddasa munanan raunuka ga waɗanda suka tsira. Jami’an ceto sun isa wurin cikin gaggawa, tare  da ɗaukar gawarwaki da miƙa wadanda suka jikkata zuwa asibiti mafi kusa domin kulawa ta gaggawa.

A halin yanzu, hukumar NYSC ba ta fitar da wata sanarwa ba kan abin da ya faru, yayin da Hukumar Kiyayeb Haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta fara bincike don gano musabbabin haɗarin da ya jefa iyalai da al’ummar jami’ar cikin alhini. Lamarin ya sake cefa tambayoyi kan lafiyar hanyoyinmu da kuma yanayin lafiyar motocin hayar da ake amfani da su wajen jigilar mutane zuwa ko’ina cikin ƙasar.

Jama’a da dama sun nuna damuwa a shafukan sada zumunta, inda malamai da ɗalibai da tsoffin ƴan NYSC ke kira ga gwamnati da hukumar NYSC su sake fasalin tsarin tura sabbin masu hidimar ƙasa, musamman wajen rage doguwar tafiya da ke jefa rayukan matasa cikin haɗari.

Wasu na ganin lokaci ya yi da za a kafa ƙa’idoji mafi tsauri kan motocin da ake haya da su don  jigilar sabbin masu yin hidimar ƙasa, tare da samar da ƙarin hanyar tafiya da tafi aminci.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *