’Yan bindiga sun kashe wani mutum sun sace hakimi a Kwara
Ana tsaka da Sallah ’yan bindiga suka harbe wani mutum har lahira sa’annan suka yi garkuwa da basarake a ƙauyen Rani Ramat da ke Ƙaramar Hukumar Patigi a Jihar Kwara.
Al’ummar yankin sun ce maharan sun kai farmaki ne a kan babura a yayin da ake Sallar Magariba ranar Lahadi inda suka rika harbi babu ƙaƙƙautawa.
A yayin da jama’a ke guje-gujen neman tsira ne ’yan bindigar suka harbe wani mutum. Daga nan suka yi awon gaba da basaraken ƙauyen mai suna Alhaji Ndako, zuwa inda ba a sani ba.
Mazauna yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun shafe sa’o’i suna cin karensu babu babbaka kafin su koma cikin daji.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Patigi, Ahmed Rufai, ya tabbatar da harin, tare da cewa mafarauta da ’yan banga sun bi sawun maharan domin ceto basaraken.
Ya bayyana cewa ƙaramar hukumar da hadin gwiwar gwamnatin jihar da jami’an tsaro na aiki tare da ’yan banga a ƙoƙarinsu na magance matsalar rashin tsaro a yankin.
Ya jaddada buƙatar fatattakar ɓata-garin daga dazukan yankin yana mai bayyana kyakkyawan fata cewa shirin gwamnatin jihar na ɗaukar jami’an tsaron dazuka da samar musu kayan aiki zai taimaka wajen shawo kan matsalar.
Wannan na zuwa ne a yayin da gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRahman, ya yi zama da masu ruwa da tsaki na ƙananan hukumomin Patigi da Edu, da nufin shawo kan matsalar tsaro da ke addabar su.