Sojoji sun kashe babban Kwamandan ISWAP, Amirul Fiya a Borno

[ad_1]



Dakarun Sojin Bataliya ta 3 da ke sansanin FOB Rann, a Ƙaramar Hukumar Kala-Balge a Jihar Borno, sun daƙile wani hari da ISWAP suka kai.

Bayan tafka artabu, sojojin sun gano gawar ’yan ta’adda uku, ciki har da babban kwamandansu, Amirul Fiya.

Sojojin sun bayyana cewa wannan nasara ta zama naƙaso ga shugabancin ISWAP a yankin.

Rundunar, ta ƙara jadadda ƙudirinta na kawo ƙarshen ta’addanci a Arewa maso Gabas.

Sojoji da sauran haɗin gwiwar jami’an tsaro na ci gaba da fatattakar ’yan ta’adda a yankin Arewa Maso Gabas.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *