Abba ya bai wa mutumin da aka kashe wa iyali kyautar kujerar hajji, gida da kuɗi

[ad_1]



Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bai wa mutumin da aka kashe wa mata da yara shida a unguwar Chiranci Dorayi, kyautar kuɗi, gida da kuma kujerar hajji.

Tallafin ya haɗa da daukar nauyin aikin Hajji da Umrah, samar masa da sabon gida, da kuma kulawar gwamnati.

Gwamnan ya kuma umarci Babban Lauyan Jihar Kano, da ya tabbatar an hanzarta gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifin.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba, bayan gwamnan ya kai wa mutumin ziyarar ta’aziyya.

Gwamna Abba ya bayyana lamarin a matsayin abin tausayi da takaici, inda ya tabbatar wa iyalin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa musu.

Ya bayar da umarnin a samar wa mutumim sabon gida, tare da jaddada cewa gwamnati za ta kula da jin daɗinsa, sannan za ta taimaka masa idan ya tashi sake yin sabon aure.

Gwamnan ya ce duk waɗanda ake zargi za a gurfanar da su a gaban kotu, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Ya ƙara da cewa zai sanya hannu kan hukuncin kisa idan kotu ta tabbatar da hukuncin, kamar yadda doka ta tanada.

Gwamnan ya yaba wa Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSS da sauran hukumomin tsaro bisa gaggawar ɗaukar mataki da haɗin gwiwa da suka yi, wajen cafke waɗanda ake zargi.

Mutumin, ya yi godiya tare da bai wa Gwamnatin Jihar Kano gidan nasa da aka kashe iyalinsa domin gina makarantar Islamiyya.

Har ila yau, Gwamnan ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalin marigayi Dokta Bature AbdulAziz, da kuma ga Baba Umar bisa rasuwar mahaifiyarsa, inda ya yi addu’ar Allah Ya jiƙansu da rahama, Ya kuma sanya su a Aljannar Firdausi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *