Gawuna ya fice daga jam’iyyar APC
[ad_1]
Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyya mai mulki ta APC a hukumance.
Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan ranar 29 ga Maris, 2026, wadda ya aike wa shugaban APC na mazaɓarsa ta Gawuna da ke ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano.
Gawuna, wanda ya yi takarar kujerar gwamnan Kano a ƙarƙashin inuwar APC a Zaɓen 2023, ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi a lokacin da yake cikinta.
Sai dai duk da cewa zuwa yanzu bai bayyana inda zai dosa ba a siyasance, amma wasu rahotanni na ci gaba da alaƙanta shi da sauya sheƙa zuwa jam’iyyar haɗaka ta ADC.
Rahotanni sun nuna cewa murabus ɗinsa na zuwa ne a daidai lokacin guguwar sauya sheƙar siyasa ke ci gaba da kaɗawa a Jihar Kano, musamman bayan ficewar tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso daga jam’iyyar NNPP zuwa ADC.
Wasu majiyoyi na cewa a kwanakin nan ana sa ran Gawuna zai gana da Kwankwaso a gidansa da ke Miller Road a Kano, abin da ke ƙara nuna alamun sabbin shirye-shiryen siyasa gabanin tunkarar zaɓen 2027.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link