Xi Ya Taya Sassou Nguesso Murnar Sake Zabensa A Matsayin Shugaban Jamhuriyar Congo
A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga Denis Sassou Nguesso bisa sake zabensa a matsayin shugaban Jamhuriyar Congo.
Xi ya ce kasar Sin da Jamhuriyar Congo suna da dangantakar abota ta tarihi mai zurfi. A shekarun baya-bayan nan, kasashen biyu sun ci gaba da karfafa amincewa da juna a fannin siyasa, sun kuma rika goyon bayan juna kan batutuwan da suka shafi manyan muradunsu da muhimman abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya, tare da samun nasarorin hadin gwiwa masu yawa a a fannoni daban-daban.
Kazalika, sun kuma sauke nauyin da ke wuyansu a matsayin kasashen da ke jagorantar dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC), inda suka taka muhimmiyar rawa wajen karfafa alakar Sin da Afirka da kuma hadin gwiwar kasashe masu tasowa. Xi ya kuma bayyana cewa zai yi aiki tare da shugaba Nguesso domin ci gaba da inganta ma’anar al’ummar Sin da Congo mai kyakkyawar makoma ta bai-daya a matakin koli, tare da bayar da gagarumar gudummawa wajen gina al’ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makoma ta bai-daya a sabon zamani. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)