Dabara Ta Rage Ga Mai Shiga Rijiya
[ad_1]
Tataburzar siyasar da ake yi game da siyasar yankin gabas ta tsakiya na ci gaba da tona asirin yadda turawan yamma ke ci gaba da cin tuwo da miyar bara. Tun daga rikicin yankin Palasdinu zuwa abubuwan da ke faruwa kwanan nan kan batun Iran, duk da a zahiri suna haifar da koma-baya, amma kuma a badini suna kara mayar da burin yammacin duniyar tamkar mafarkin da ba zai taba zama gaskiya ba saboda kiyayyarsu da take karuwa a zukatan al’ummomin yankin.
Bayan harin Amurka da Isra’ila na shekarar 2025 da gajeren rikicin da ya biyo baya, wasu masana sun lura cewa maimakon hakan ya raunana Iran daga zuci, sai ya kara mata kwarin gwiwar karfafa matsayinta na tsaro tare da kara zurfafa dangantakarta ta diflomasiyya musamman da manyan kasashe masu fada-a-ji a yankin Asiya.
Fankamar yammacin duniya ita ce karfin tattalin arziki da kuma makamai. Amma kuma yaki daga zuciya ake cin nasararsa. Ko an zubar da jini, wutar gaba mai ruruwa a zukatan al’umma ba ta mutuwa, sai dai ta sake rincabe nasarar da aka ci. Ga misalai nan a kasashen da Amurka da kawayenta suka afka musu, kamar Afghanistan, Iraqi da Libiya da kuma sauran kasashen da suka yi musu munakisa.
Duk da cewa takunkuman da aka kakabawa Iran sun lalata tattalin arzikinta kuma sun shafi rayuwar talakawan kasar, amma kuma ba su samar da tasirin siyasa da Washington ta yi tsammani ba. A halin yanzu, galibin fushin da al’ummar Iran ke yi bisa yanayin da aka jefa su ciki na kara karkata zuwa ga wadanda suka kakaba takunkuman duk kuwa da zanga-zangar da aka yi kwanan baya, saboda haka, matsin tattalin arzikin yammacin duniya bai ba su asalin muradin abin da suke nema ba.
A wani tsokaci da ya yi ta kafar sada zumunta, wani farfesa daga tsangayar nazarin muhalli ta Jami’ar BUK dake Nijeriya, Malam Aliyu Salisu Barau ya yi nuni da cewa, ya kamata kasashen yammacin duniya su fahimci rashin tasirin dabi’ar tilastawa a wannan zamani, inda ya kafa hujja da cewa, sassauta takunkumi da inganta yanayin jin kai na iya sauya ra’ayoyin al’umma fiye da tayar da husuma. Kazalika, kyakkyawar diflomasiyya da hulda ta tattalin arziki na iya samar da yanayi mafi dacewa na ci gaba da kuma zaman lafiya na dogon lokaci.
A halin yanzu dai yanayin daidaiton karfin duniya ya sauya sosai ta fuskar wayewa hatta ma da ci gaban tattalin arziki, misali a shekarar 2000, tattalin arzikin Tarayyar Turai ya ninka na kasar Sin sau da yawa, amma zuwa 2025 sun yi kusan kafada da kafada. Kuma hasashe ya nuna cewa zuwa 2050 tattalin arzikin Sin zai iya ninka na Turai sau biyu. Wannan sauyi, a cewar masu sharhi, alama ce ta sake daidaita tasirin duniya a dogon lokaci, kuma yana kalubalantar tsoffin tsare-tsare na kashin dankali dake jagorantar manufofin yammacin duniya. Don haka batun samun sauyi mai ma’ana babu makawa, yanzu dabara ta rage ga mai shiga rijiya! (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link