Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana ’Yan Bindiga A Matsayin ’Yan Ta’adda
[ad_1]
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a matsayin ’yan ta’adda a hukumance.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ne, ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka yi a Abuja.
- Masanin Kasar Afirka Ta Kudu: Hadin-Gwiwar Sin Da Afirka A Bangaren Kimiyya Da Fasaha Na Kawo Sauye-Sauye Ga Tattalin Arzikin Afirka
- An Kama Mata 2 Bisa Zargin Shigar Da Miyagun Ƙwayoyi Gidan Gyaran Hali Na Kano
Ya ce daga yanzu, duk wani mutum ko ƙungiya da ke ɗauke da makamai suna sace mutane ko tsoratar da jama’a, za a ɗauke su a matsayin ’yan ta’adda.
Ministan ya ce wannan mataki yana nuna cewa gwamnati za ta ɗauki mataki mai tsauri ba tare da sassauci ba.
Ya ƙara da cewa hukumomin tsaro za su ƙara haɗin gwiwa da musayar bayanan sirri domin ɗaukar mataki cikin gaggawa.
Gwamnatin ta kuma ce za ta tura jami’an tsaro na musamman zuwa dazuka da yankunan karkara domin hana ’yan ta’adda samun mafaka.
Matakin na zuwa ne yayin da matsalar satar mutane da rashin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a sassan ƙasar.
[ad_2]
Source link