Yadda Jigo A APC Na Kano Ya Rasu A Otal A Abuja

[ad_1]

Rahotonni da jaridar Aminiya ta yau da kullun ta samu, sun bayyana yadda Mataimakin Sakataren Shirye-shirye na jam’iyya APC a Jihar Kano, Abdulsalami Ginsau, ya rasu a otal din ‘Chida Hotels’ da ke unguwar Utako a Abuja.

Ginsau, wanda lauya ne, shi ne shugaban kwamitin da aka dorawa alhakin shirya masauki ga wakilan Jihar Kano zuwa babban taron APC da aka kammala kwanan nan a Abuja.

  • Me Ya Sa Kungiyar Tattara Bayanai Ta Kasa Da Kasa Ta Samu Mazauni A Birnin Beijing?
  • Bahallatsar Gabas Ta Tsakiya: Sin Da Pakistan Sun Ba Da Mafita

An ruwaito cewa, ya rasu ne a ranar Juma’a, 27 ga Maris, bayan da ake zargin ya makale a cikin lif mai matsala da ke a otal din.

Da yake magana kan lamarin a jiya Laraba, shugaban APC na Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya ce a matsayinsa na wanda aka dorawa alhakin shirya masauki ga wakilai, Ginsau ya iso Abuja tun kwana guda kafin taron domin tanadar dakuna ga mahalarta daga jihar.

Ya ce bayan ya kammala tanadar masaukin wakilan, Ginsau sai ya sauka a otal din Chida. Doguwa ya kara da cewa sun fara zargin akwai matsala ne lokacin da ba su ga Ginsau ba a wurin taron ranar Juma’a, lamarin da ya sa suka fara nemansa cikin gaggawa.

Ya ce yayin da suke cigaba da nemansa a sassa daban-daban na Abuja, sun je ofishin ‘yansanda na Utako domin kai rahoto, inda aka sanar da su cewa an samu wani rahoto na rasuwa a otal din Chida.

Doguwa ya ce da suka isa otal din, sun gano gawar mamacin, inda suka tabbatar cewa shi ne Ginsau. Ya danganta faruwar lamarin da abin da ya kira sakacin mahukuntan otal din.

A cewarsa, wasu wakilai da ke sauke a otal din tare da mamacin sun riga sun bayyana damuwa cewa lif din otal din na da matsala. Ya ce an kai gawar mamacin domin gudanar da binciken gawa (autopsy), don haka, yanzu suna tsumayin sakamakon binciken da ‘yansandan ke yi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *