Kamfanonin Sin Masu Saurin Bunkasa Sun Kai Kaso Daya Bisa Uku Cikin Jimillar Makamantansu Na Duniya
[ad_1]
Wani jadawali mai kunshe da jerin sabbin kamfanonin duniya masu saurin samun ci gaba na shekarar 2025, ya nuna yadda irin wadannan kamfanoni masu helkwata a Sin, suka kankane sama da kaso daya bisa uku na jimillar na duniya baki daya, matakin da ya shaida damar dake akwai a kasar ta Sin, ta cin gajiya daga sabbin fasahohi, irinsu fasahohin sarrafa halittu masu rai ko “biotechnology”, da na kirar na’urorin harhada kayan laturoni na “semiconductors”.
Wani rahoto na shekarar 2025 daga cibiyar bincike ta Hurun, ya fayyace alkaluma dake nuna cewa, cikin kamfanonin kasa da kasa 819 da aka tattara bayanan su, adadin wadanda mai yiwuwa darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan daya cikin shekaru uku, 278 kamfanoni ne na kasar Sin, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 8 bisa dari a mizanin shekara-shekara, kana hakan ya sanya Sin din zama kasa ta biyu a bayan Amurka, wadda ta samu koma bayan kaso 8 bisa dari. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link