Kamfanonin Finland: Sin Za Ta Zama Babban Injin Samar Da Ci Gaba A Gare Mu
[ad_1]
Gungun ‘yan kasuwar kasar Finland sun iso kasar Sin, yayin ziyarar firaministan Finland Petteri Orpo zuwa kasar ta Sin. A lokacin taro na 6 na kwamitin hadin gwiwar kamfanoni masu kirkire-kirkire na Sin da Finland da ya gudana a ranar Litinin 26 ga watan nan a birnin Beijing, kamfanonin kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwar kasuwanci da dama.
Burin karkata zuwa ga fasahohin dijital, da raya makamashi mai tsabta, da rage fitar da hayaki mai dumama yanayi, da kiwon lafiya da sauransu, sun zamo muhimman batutuwan da aka tattauna a wajen taron. ‘Yan kasuwar Finland sun nuna kwarin gwiwa matuka kan kasuwar Sin, yayin da amincewa da damammakin Sin ya zama matsaya daya da kamfanonin na Finland suka cimmawa. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link