Babu Wata Tanka Da Ta Sauka A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Jihar Legas A Ranar Juma’a —NPA
[ad_1]
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA ta sanar da cewa, babu wani jirgin ruwa daya daga cikin Jiragen da ake jira guda 10, da ake tsimayi da ya sauka a Tashoshin Lekki, Tincan da ta Apapa, a ranar Juma’ar da ta gabata.
NPA ta sanar da haka ne, a wani sako, da wallafa, wanda ta ce, Jiragen Ruwan guda 10, da ake tsimayi na dauke ne da Buhunhunan takin zamani, samfarin urea da Kwantainoni da Dayen Mai da Buhunhunan Alkama da wasu Kwantainoni, da basa dauke da komai a cikinsu, sai kuma Kifi.
- Majalisar Dattawa Ta Kai Ta’aziyya Ga Al’ummar Kurmin Wali, Ta Yi Alkawarin Kayan Agaji
- Dambarwar Da Ta Biyo Bayan Sauya Sheƙar Gwamna Yusuf Na Jihar Kano
A cewar sakon, kayan da ake tsimayi da za a yo jigilarsu a cikin Jiragen Ruwa guda 26 da ke dauke da Man Fetur da kayan abinci da sauransu, ana sa ran za su sauka a Tashohin jihar Legas ne, daga ranar 23 zuwa ranar 31, na watan Janairun 2026
A kwanan baya, an ruwaito cewa, Jiragen Ruwa guda 21, dauke da kaya da suka hada da, Kwantaina da Man Dizil da Buhunhunan takin urea, da Buhunhunan Suga da Gishiri da sauransu, za su sauka a Tashoshin, na jhar Legas.
[ad_2]
Source link