’Yan bindiga sun kashe ɗan kasuwa, sun sace matarsa a Bauchi

[ad_1]



Ana zargin wasu ’yan bindiga da kashe wani fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Muhammad Bakoshi, lokacin da suka kai hari garin Zalau da ke Ƙaramar Hukumar Toro a Jihar Bauchi.

Bayan kai hari, sun sace ɗaya daga cikin matansa, Hannatu Muhammad.

Wani mazaunin yankin, Shamsuddeen Hashimu Zalawa, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun je gidan mutumin da tsakar dare.

Ya ce sun dinga harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici.

Ya ƙara da cewa sun nufi gidan Bakoshi kai-tsaye, wanda hakan ya sa wasu ke zargin ko turo su aka yi.

Ɗan kasuwar mutum ne da ke taimakon jama’a musamman a sha’anin tsaro da kuma sabgogin maharba.

Haka kuma, ya kasance jami’in ladabtarwa a ƙungiyar First Aid ta JIBWIS a Zalau.

Zalawa, ya ce Bakoshi yana da mata biyu.

’Yan bindigar sun tafi da babbar matarsa, yayin da suka bar ƙaramar matarsa wacce ba ta jima da haihuwa ba.

Ƙoƙarin jin karin bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi, bai yi nasara ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *