Ƴan Bindiga Sun Kashe Ƴansanda 5 A Bauchi
[ad_1]
Ƴan bindiga sun hallaka jami’an ƴansanda biyar tare da jikkata biyu a wani harin kwantan ɓauna da ya afku a ƙauyen Sabon Sara, cikin ƙaramar hukumar Darazo ta Jihar Bauchi. Wani ganau ya tabbatar cewa harin ya faru ne yayin da jami’an ke gudanar da sintirin domin daƙile rikicin manoma da makiyaya a yankin.
Jami’an da suka rasa rayukansu sun haɗa da DSP Ahmad Muhammad na sashin bincike (SID), da ASP Mustapha Muhammad na 10 PMF, da Sufeto Amarhel Yunusa na 10 PMF, da Sufeto Idris Ahmed na 10 PMF, da Kufural Isah Muazu na AKU. Biyu daga cikin jami’an, Sufeto Isah Musa da Sufeto Yusuf Gambo daga sashin SID, sun samu munanan raunuka bayan harin.
Kakakin rundunar ƴansanda ta jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce an samu rahoton ɓullar wasu da ake zargin na ɗauke da makamai a yankin a ranar 22 ga Nuwamban 2025. Bayan rahoton, an tura tawagar haɗin gwuiwa wacce ta ƙunshi RRS, da 10 PMF, da AKU, da SID da jami’an sintiri don gudanar da aikin a asirce. Sai dai yayin sintirin ne aka yi musu kwantan ɓauna, lamarin da ya haddasa musayar wuta mai tsanani tsakanin ɓarayin dajin da jami’an tsaro.
Rundunar ta tura ƙarin jami’ai domin ceto waɗanda suka shiga harin tare da kwashe gawarwaki da waɗanda suka jikkata zuwa babban asibitin Darazo. Wakil ya tabbatar da cewa nan gaba kaɗan za a cafko waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki, tare da sake shiri wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Kwamishinan ƴansanda na jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya kai ziyarar gani da ido zuwa wurin faruwar lamarin, inda ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu, tare da sake jaddada ƙudirin rundunar wajen ci gaba da kare al’umma daga barazanar ƴan bindiga.
[ad_2]
Source link