‘Yansanda Sun Ceto Mutane 7 Daga Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara
[ad_1]
Rundunar ‘Yansandan Jihar Zamfara ta ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su bayan wani harin ‘yan bindiga na cikin dare a karamar hukumar Gusau.
Lamarin ya faru da misalin karfe 11 na dare a ranar 25 ga Maris, lokacin da ‘yan bindiga dauke da muggan makamai suka kai hari gidan Muhammad Lawal da ke Nasarawa, Gundumar Damba. Maharan sun sace matarsa tare da ‘ya’yansa shida a cikin wani mummunan hari mai ban tsoro.
- Wata Ƙungiya Ta Mara Wa Ganduje Baya Don Zama Daraktan Kamfen Ɗin Tinubu A 2027
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 5 A Sokoto Da Zamfara, Sun Ƙwato Makamai
Sai dai cikin gaggawa, babban jami’in ‘yansanda na yankin (DPO) ya tura tawagar sintiri zuwa wurin da abin ya faru. Jami’an sun yi artabu da maharan da ke kokarin tserewa, inda aka yi musayar wuta mai zafi, lamarin da ya tilasta wa ‘yan bindigar barin wadanda suka sace tare da guduwa don neman tsira.
A halin yanzu, an ceto dukkan mutanen bakwai ba tare da wani rauni ba, kuma an mayar da su lafiya zuwa ga iyalansu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda, Yazid Abubakar, ya ce rundunar na ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar.
[ad_2]
Source link