Remi Tinubu ta ƙaddamar da Asibitin Koyarwa na Tarayya a Gombe

[ad_1]



Uwargidan Shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da sabon Asibitin Koyarwa na Tarayya (FMC) da aka gina a garin Kumo, Ƙaramar hukumar Akko ta Jihar Gombe

An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne tare da halartar Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya da kuma Ministan Kula da Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Ali Pate.

A jawabinta, uwargidan shugaban Ƙasar ta ce wannan asibiti na nuna sakamakon jagoranci irin na hangen nesa ƙarƙashin shirin Sabunta Kasashen Duniya na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ta ce, asibitin zai ƙara inganta damar samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar Jihar Gombe da ma maƙwabtan jihohi, tare da zama shaida ga jajircewar Gwamnatin Tarayya wajen kyautata rayuwar ’yan ƙasa.

“Ina da yaƙinin cewa, Gwamna Inuwa Yahaya wanda yake da ƙaunar al’ummarsa, zai ci gaba da tallafa wa shirye-shiryenmu domin amfanin ’yan Najeriya musamman waɗanda ke karkara,” in ji ta.

Jim kaɗan, Uwargidan shugaban ƙasar ta ƙaddamar da wasu asibitoci a fadar Jihar da suka haɗa da asibitin mata da yara da ke unguwar Malam Inna da kuma kai ziyara Asibitiin Mata da Yara na Zainab Bulkachuwa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *