Rashin Tsaro: Za A Tura Rundunar Soji Ta Musamman Zuwa Kwara Da Neja – CDS
[ad_1]
Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya ce za a tura rundunar sojoji ta musamman zuwa Jihar Kwara da wasu sassan Jihar Neja domin magance matsalar rashin tsaro a yankin Arewa ta Tsakiya.
Ya bayyana hakan ne yayin gabatar da bitar kasafin kuɗin 2025 da kuma ƙudirin kasafin 2026 a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai.
- Budurwa Ta Tsere Da Motar Saurayinta Bayan Sun Kwana A Otel A Abuja
- Tsaro: Kwamitin Majalisar Ƙasa Ya Yi Watsi Da Kasafin Kuɗin Rundunar Sojin Sama Na 2026
Oluyede ya ce sojoji sun samu nasarori wajen yaƙar ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane, amma domin ɗorewar zaman lafiya dole ne a ƙara ƙarfafa rundunar ‘yansanda da Hukumar NSCDC domin su riƙe yankunan da aka ƙwato.
Ya kuma ce an riga an tura runduna ta musamman zuwa jihohin Benuwe da Filato, sannan za a ƙaddamar da wata sabuwar rundunar haɗin gwiwa mai suna Operation Savannah Shield domin aiki a Kwara da wasu sassan Neja.
Babban hafsan ya ƙara da cewa sojoji na fuskantar ƙarancin ma’aikata, don haka akwai buƙatar ƙarin haɗin kai da isasshen tallafi domin inganta tsaro a faɗin ƙasar.
[ad_2]
Source link