NiMet ta yi hasashen faɗuwar damuna da wuri bana a Kano, Jigawa da wasu jihohi 12
[ad_1]
Hukumar Hasashen Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta yi hasashen cewa a bana damuna za ta fadi da wuri a sassan jijohin Kano, Jigawa da Katsina, sabanin yadda aka saba gani a shekarun baya.
Kazalika, hukumar ta ce ruwan sama zai fara da wuri a jihohin Ribas, Bayelsa, Akwa Ibom, Kuros Riba, Binuwai, Kogi, Nasarawa, Oyo da kuma wasu sassan Kebbi, Neja, Adamawa da Taraba.
Hukumar ta kuma yi hasashen cewa ruwan sama zai dan yi jinkiri a Jihar Borno, tana gargadin cewa ruwan da aka gani a wasu sassan ƙasar ba ya nuna faduwar damina ba ne, illa kawai “damunar karya” ce.
Da yake jawabi a wajen taron hasashen yanayi na shekara ta 2026 a Abuja, Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya ce, “Mun riga mun ga wasu manyan ruwan sama a sassan kudancin ƙasar nan a bana.
“Ina so in jaddada cewa wannan ba yana nufin damina ta fadi ba ne. Waɗanda ke yin noma da sauran ayyukan da ke dogara da ruwan sama su koma ga hasashen da aka fitar ko su tuntubi NiMet don samun Karin bayani.”
NiMet ta kuma ce ruwan sama zai dauke da wuri fiye da yadda aka saba gani a wasu sassan Ogun, Osun, Ondo, Imo, Ribas, Akwa Ibom, Kogi da Neja, yayin da Lagos, Anambra, Enugu, Kuros Riba, Binuwai, Nasarawa da Kaduna za su fuskanci jinkiri a ƙarshen damina.
Hukumar ta kuma yi hasashen cewa za a sami tsawon damina fiye da yadda aka saba a jihohin Legas, Binuwai, Enugu, Ebonyi, Ogun, Oyo, Nasarawa, Anambra, Kwara, Kebbi, Kaduna, Gombe da Taraba, yayin da wasu sassan Borno, Yobe da Neja za su fuskanci gajeriyar damina.
Ministan ya kuma yi gargadin cewa za a sami tsananin fari tsakanin watan Maris zuwa Mayu a jihohin Oyo da Ogun, yayin da matsakaicin fari zai shafi Ekiti, Kogi, Osun, Ondo, Edo, Ebonyi, Abia, Kuros Riba, Delta da wasu sassan Kwara.
A tsakanin watannin Yuni zuwa Agusta kuwa, hukumar ta yi hasashen tsananin fari da zai iya ɗaukar kwanaki 21 a Bauchi, Borno, Gombe, Jigawa, Katsina, Kano, Kebbi, Kwara, Nasarawa, Niger, Oyo, Filato, Sakkwato, Yobe da Zamfara.
Game da karamin lokacin farin kuwa, NiMet ta ce zai fara a ƙarshen watan Yuli kuma zai yi tsanani a Lagos, Ogun, Ekiti da wasu sassan Oyo, inda zai iya ɗaukar kwanaki 28 zuwa 40. Matsakaicin tasiri kuma zai shafi Ondo, Kwara da Edo.
Hukumar ta kuma yi hasashen cewa zafin rana da dare zai fi wanda da aka saba da shi a yawancin sassan ƙasar a watan Janairu, Fabrairu, Maris da Mayu 2026.
Daraktan Hukumar NiMet, Farfesa Charles Anosike, ya ce hukumar ta ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnati da kungiyoyin ƙasa da ƙasa wajen sauƙaƙa wannan hasashen ga manoma a fadin kasar.
“Muna aiki tukuru don hanzarta samar da yanayi na shawarwarin zamani tare da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa,” in ji shi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link