’Yan sanda sun daƙile harin ɓarayin shanu a Zamfara
[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta samu nasarar daƙile harin ɓarayin shanu a a yankin Damba da ke Jihar.
Kakakin rundunar Yazid Abubakar, ya bayyana cewa maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 2:20 na daren ranar Alhamis.
Rundunar ta bayyana cewa maharan, waɗanda ake zargin ɓarayin shanu ne, sun kai hari wani babban garken shanu a unguwar Tsunami, gundumar Damba, kusa da Gusau.
Kakakin cikin wata sanarwa da ya fitar a Gusau, ya ce nan da nan jami’an rundunar suka kai ɗauki yankin bayan samun rahoton aukuwar harin.
Ya ƙara da cewar jami’an rundunar sun yi nasarar daƙile harin tare da fatattakar maharan.
DSP Yazid ya ƙara da cewa rundunar ta nuna jarumta da ƙwarewa inda suka yi nasarar fatattakar ɓarayin shanun.
“An samu nasarar daƙile harin ɓarayin shanu tare da mayar wa masu shanun gaba ɗaya cikin nasara,” in ji Yazid.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Maikaba, ya yaba da ƙwazon jami’an da ƙwarewar da suka nuna.
Kwamishinan ya ƙara da yin kira ga al’umma su ci gaba da bai wa rundunar haɗin kai da goyon baya wajen bayar da sahihan bayanai domin daƙile ayyukan ’yan ta’adda a faɗin jihar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link