Sin Ta Lissafa Nasarorinta Na Binciken Samaniya A 2025 Inda Ta Harba Kumbuna 92 Da Karin Wasu Ayyuka
[ad_1]
Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar da sanarwar kididdigarta game da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar ta shekarar 2025 a yau Asabar, inda ta nuna cewa, fannin fasahar kasar Sin ya samu tagomashi a shekarar 2025, inda kudaden da aka kashe a bangaren kere-keren manyan fasahohin da gudanar da bincike, suka karu sosai.
Rahoton ya ce, an samu karuwar sarrafa kayayyakin da manyan masana’antun fasahohin zamani ke fitarwa da kashi 9.4 cikin dari a mizanin shekara-shekara, yayin da ribar da kamfanoni masu alaka da hakan suka samu ta haura kashi 13.3 cikin dari.
Nasarorin da aka cimma a bangaren sararin samaniya kuwa sun yi fice a cikin kididdigar. A shekarar 2025, kasar Sin ta kammala harba kumbuna har guda 92, ciki har da na ayyukan kasuwanci guda 50. An samu ci gaba a fasahar kera roka da za a iya sake amfani da ita, inda Zhuque-3 da Long March-12A suka yi tashinsu na farko kuma suka yi nasarar aikowa da sassansu bisa mataki na biyu na zuwa da’irar sararin samaniya.
A fannin fasahar zamani da na soja kuwa, rahoton ya nuna cewa, an kaddamar da jirgin Fujian, jirgin ruwa na yaki na farko mai dauke da fasahar majajjawar maganadisu mai amfani da lantarki da kasar Sin ta kera a cikin gida.
A cewar rahoton, a bangaren fasahar kirkirarriyar basira kuma, manhajar neman bayanai ta DeepSeek da aka kera a cikin gida ta ja hankalin duniya. Har ila yau, kasar Sin ta gudanar da gwajin farko na fasahar da za ta ba da damar sadarwa kai-tsaye tsakanin kwamfuta da kwakwalwar dan’adam.
Adadin kudin da kasar Sin ta kashe kan bincike da samar da ci gaba a shekarar 2025 ya kai yuan tiriliyan 3.93 (kimanin dala biliyan 569), wanda ya karu da kashi 8.1 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2024. Kasar ta kuma ba da takardun izini na hakkin mallakar kirkira guda 972,000 a cikin shekarar, wanda ke nuna ci gaba da kokarin karfafa sashen kirkira na kasar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link