Ko Za A Ga Sauyi Bayan Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka?
[ad_1]
Tawagogin Sin da Amurka sun fara gudanar da tattaunawa a karo na 6, kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya, jiya Lahadi a birnin a Paris na Faransa, a wani lokaci da harkokin cinikayya a duniya ke cikin yanayi na hargitse saboda matakan son kai da Amurka ke dauka.
Yayin da kasar Sin ke fadada bude kofarta da kara gyara manufofi ta yadda za ta samar da kyakkyawan muhallin kasuwanci da na ci gaba ga ’yan kasuwa da masu zuba jari na kasashen waje, a daya bangaren, Amurka na ci gaba da bullo da matakan kariyar cinikayya.
A baya-bayan nan, an ji yadda Amurka ta sanar da kaddamar da bincike mai lamba 301 kan kasashe da yankuna 60, ciki har da kasar Sin, bisa hujjojin rashin daukar mataki kan “Tilasta Kwadago” da “Fitar da Kayayyaki Fiye da Kima”.
Irin wadannan matakai da Amurka ke ci gaba da bullowa da su daya bayan daya, suna mayar da hannun agogo baya kan irin ci gaban da ake samu da kuma kara hargitsa tsarin cinikayya da haifar da rashin tabbas a duniya.
Abun da ya kamata ta yi la’akari da shi shi ne, yayin da take kokarin durkusarwa ko dakile abokan cinikayyarta, to tana kara durkusar da kamfanoninta na ci gida, kuma hakan ba zai kai ta ga cimma burinta ba. Misali, wani sakamakon bincike na babban bankin Amurka ya ce, masu sayayya da masu harkokin kasuwanci ne suka biya kaso 90 na haraje-harajen da Amurka ta kakkaba bara. Har ila yau, wani rahoto na cibiyar JP Morgan ya ruwaito cewa, masu matsakaitan kamfanoni a Amurka ne suka fi jin jiki sanadiyyar matakan haraji na kasar.
Babban misali da ya yi hannun riga da Amurka shi ne manufofin kasar Sin. Tana kara bude kofa da saukaka matakan cinikayya ga baki, amma kuma wannan bai sa ta ragu da komai ba, sai ma karin ci gaba da tagomashi da take samu. Wasu alkaluma da hukumar kididdga ta Sin ta fitar yau Litinin sun nuna yadda harkokin tattalin arziki suka samu tagomashi a farkon bana tsakanin Junairu da Fabrairu, inda karuwar manyan masana’antun kasa ya kai kaso 6.3 bisa dari, ma’aunin samar da sana’ar bayar da hidima ya karu da kaso 5.2, yawan kayayyakin yau da kullum da aka sayar ya kai kudin Sin yuan biliyan 8607.9, karuwar kaso 2.8 bisa dari, dukkansu idan aka kwatanta da makamancin lokaci a bara.
Ya zama wajibi Amurka ta lura cewa, babu inda rikici zai kai ta. Ya kamata kamar yadda ake da kyakkyawan fata game da tattaunawar karo na 6, a ga sauyi daga gare ta bayan kammaluwarsa. Sauyi mai aminci da dorewa da bangarorin biyu za su kara cin gajiyarsa, har ma da sauran sassan duniya. (Fa’iza Mustapha)
[ad_2]
Source link