Tinubu zai tafi ziyarar aiki Birtaniya ranar Talata
[ad_1]
A gobe Talata ce ake sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu, zai bar birnin Abuja domin kai wata ziyarar aiki Birtaniya bisa gayyatar Sarkin Ingila, Charles III da matarsa Sarauniya Camilla.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Ya ce Tinubu zai tafi tare da uwargidansa, Oluremi Tinubu da wasu manyan jami’an gwamnati domin ƙarfafa alaƙar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Birtaniya, musamman a fannoni kamar kasuwanci, zuba jari, ƙaura, da musayar al’adu.
A cewar sanarwar, Sarkin Charles III zai karɓi baƙuncin shugaban Najeriya da matarsa a Windsor Castle daga ranar 18 zuwa 19 ga Maris, inda za su halarci wani baje kolin kayayyakin al’adun sarauta da ke da alaƙa da Najeriya.
Sanarwar ta ce wannan ita ce ziyarar farko da wani shugaban Najeriya zai kai Birtaniya cikin shekaru 37, kuma Tinubu ne shugaban Najeriya na farko da Sarkin Ingila zai karɓa a Windsor Castle.
Haka kuma, shugaban zai halarci wani zaman rattaba hannu kan yarjejeniyar tallafin kuɗi ta fam miliyan 746 tsakanin Hukumar Kula da Fitar Kudi Ketare ta Birtaniya da Hukumar Tashoshin Ruwan Najeriya da kuma Maaikatar Kudi ta Najeriya, domin gyara manyan tashoshin jiragen ruwa guda biyu a Najeriya, duk a Jihar Legas.
A yayin ziyarar, Tinubu zai gana da Firaministan Birtaniya Keir Starmer a Fadar Downing Street, inda ake sa ran za su tattauna kan faɗaɗa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.
Ana kuma sa ran ziyarar shugaban na Najeriya za ta ƙare da rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da dama da suka shafi kasuwanci, zuba jari, tsaro da haɗin gwiwar al’adu.
Daga cikin tawagar da za ta rakiyar shugaban ƙasar akwai Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Ministan Shari’a Lateef Fagbemi, Ministan Ma’adanai Dele Alake, Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris, da Ministan Kuɗi Wale Edun, da sauran manyan jami’an gwamnati.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link