Abubukar Malami zai ci gaba da zama a komar EFCC

[ad_1]



Wata babbar kotun birnin tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Alhamis, ta yi watsi da buƙatar neman belin tsohon babban Lauyan ƙasar kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami, na neman a sake shi daga hannun Hukumar yaƙi da masu yi wa ƙasa zagon ƙasa ta EFCC.

Mai shari’a Babangida Hassan ya ce, ba zai iya bayar da neman belinsa ba saboda kotun ƙoli ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare tsohon Ministan domin ci gaba da bincike.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Malami, jigo ne a jam’iyyar adawa, kuma mai neman tsayawa takarar Gwamna a Jihar Kebbi, ya kasance a hannun Hukumar EFCC tun a makon jiya a kan zargin karkatar da kuɗaɗe.

Malami, wanda ya nemi belin ta hannun lauyansa, Sulaiman Hassan, babban lauyan Najeriya ya garzaya kotu yana neman belin daga hannun Hukumar EFCC.

Tsohon Ministan ya bayyana cewa, tsare shi da Hukumar ke yi, ya sabawa doka.

Sai dai lauyan EFCC, Jibrin Okutepa wanda kuma babban lauya ne a Najeriya, ya gabatar da cewa hukumar EFCC na tsare da tsohuwar ministar ne ta hanyar bayar da umarnin ci gaba da tsare shi da aka samu a wata babbar kotun babban birnin tarayya Abuja da mai shari’a S.C Oriji ya bayar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *