Gobara ta yi ta’adi a Kasuwar Kumo da ke Gombe
[ad_1]
Wata mummunar gobara da ta tashi da misalin ƙarfe 2:00 na dare a ranar Lahadi, a babbar kasuwar Kumo da ke ƙaramar hukumar Akko a Jihar Gombe, ta haddasa asarar dukiya mai tarin yawa ga ’yan kasuwa.
Gobarar ta cinye manyan shagunan kontena da na tireda da ke cike da kayayyaki, tare da shagunan sayar da kayan miya da sauran kayayyakin kasuwanci, lamarin da ya jefa ’yan kasuwar cikin damuwa da tashin hankali.
Shaidun gani da ido sun shaida wa wakilinmu cewa wutar ta tashi ne cikin dare da ƙarfi, inda ta lalata rumfunan ’yan kasuwa da dama tare da kayayyakin da ke cikinsu.
Sun ce ɓarnar ta yi muni matuƙa, domin shagunan da wutar ta shafa sun ƙone ƙurmus, ba tare da an samu damar ceto wani abu ba.





Wani mazaunin garin Kumo, Abubakar Kumo, ya bayyana cewa har zuwa lokacin da gobarar ke ci ba a samu isowar jami’an kashe gobara ba, lamarin da ya sa al’ummar gari suka riƙa amfani da ruwa da sauran dabaru wajen shawo kan wutar.
A cewarsa, taimakon Allah ne ya sa aka samu kashe gobarar kafin ta bazu zuwa sauran sassan kasuwar, wanda hakan ya hana aukuwar asara mafi girma.
Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, sai dai jama’a na kiran hukumomin da abin ya shafa da su ƙara ɗaukar matakan kariya da gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasuwa nan gaba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link