CGI Babandede Mai Ritaya A Mizanin Kyawawan Halaye Da Kwazon Aiki

[ad_1]

Idan aka dora kyawawan halaye da kwazon aikin tsohon shugaban hukumar shige da fice ta kasa (NIS), CGI Muhammad Babandede mai ritaya, a mizani, za a ga cewa ya kasace kwararren masanin tsaron iyakoki, sannan masani a harkokin kula shige da fice.

Ya kasance mai fafutuka don tsaron iyakokin kasar nan na tsawon shekaru arba’in na aikin gwamnati. Haka kuma ya kasance mashahurin mai fafutuka wajen kawar da talauci, rashin abinci mai gina jiki a cikin iyalai da kuma yaki kan matsalar yara da ba sa zuwa makaranta.

  • Fasahar Electronic Call-up Da NPA Ta Wanzar Ta Samar Da Sauki —Tsohon Kwaminsihan Sufuri
  • Babu Wata Tanka Da Ta Sauka A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Jihar Legas A Ranar Juma’a —NPA

Ya kasance mamba na hukumomi da dama kuma ya kasance shugaban gidauniyar ‘Peace Build-ing Debelopment Foundation’, gidauniyar da ba ta neman kudin shiga da ke koyarwa, horarwa da yin fafutuka don zaman lafiya da tsaro a duniya baki daya.

Har ila yau, ya kasance shugaba kuma wanda ya kafa gidauniyar Sure4U, gidauniyar da ba ta neman kudin shiga, wadda ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen tallafa wa yara da ba sa zuwa makaranta da mutane masu rauni musamman a arewa maso yamma, musamman a ji-hohin Kano da Jigawa da kuma Abuja.

Nijeriya a yau fiye da kowane lokaci tana bukatar CGI Muhammad Babandede mai ritaya, idan Allah sa ya rike mukaman siyasa da suka hada da kujerar Sanata na Jigawa ta arewa maso gabas a yankinsa na asali, to al’umma za su samu wakilci nagari.

Tsaron cikin gida na Nijeriya shi ne abu mafi muhimmanci a zuciyar Muhammad Babandede, wannan za a iya tabbatar da shi, daga yadda ya jagoranci hukumar shige da fice ta kasa, loka-cin da aka nada shi a matsayin shugabana hukumar shige da fice na 16 a shekarar 2017, karkashin mulkin shugaban kasa Muhammad Buhari. Ya jagoranci kafa rundunar kula da iyakokin kasar nan tare da kafa sassanoni da dama a jihohin iyaka masu muhimmanci a Nijeri-ya a yankin kudu maso yamma da suka hada da Legas, Oyo da Ogun, a arewacin kasar kuma sun hada da Katsina, Kebbi, Sakkwato, Kano, Jigawa, a kudu maso kudu kuwa sun hada da Akwa Ibom, Krus Ribas, da yawan jami’an rundunar kula da iyakoki da ke aiki a zamaninsa ba sa dogaro da kwamandojin jihohi ba a manyan iyakokin kasa.

A karkashin kulawarsa, fasfo na Nijeriya ya koma na zamani mai inganci a shekarar 2018, wan-da ya sanya Nijeriya ta zama ta farko a Afrika, ya yi aiki tare da rundunar ‘yansandan Nijeriya don kafa hadin gwiwar tsaro mai ma’ana da tsarin sadarwa tare da hada manhajar SLTD na hukumar shige da fice ta Nijeriya a karkashin jagorancinsa wanda ya samu nasarori a mafi ya-wan shari’o’i, musamman ga ‘yansadar kasa da kasa ta INTERPOL ta hanyar NCB har zuwa yau, yana amfani da kayan aikin INTERPOL NCB I-24/7 na rundunar ‘yansandan Nijeriya tare da had-in gwiwar hukumar shige da fice ta Nijeriya don kula da takardun tafiya da aka sace ko aka rasa a duk fadin duniya don tabbatar da tsaro a duniya.

Muhammad Babandede ya sadaukar da shekarunsa masu yawa wajen yi wa kasa hidima ta hanyar aikin gwamnati. Bayan ya yi ritaya ya kafa wata gidauniya wacce aka fi sani da Sure4U, ta hanyar fara fafutukar samar da ilimi kyauta karkashin shirin daukar nauyin karatun dalibai, yana fafutukar sake komar da yaran da suka fita daga makaranta a arewa da tallafa wa rukunin matane masu rauni daga cikin al’umma, har ma yana jagorantar yaki da safarar mutane ba bisa ka’ida ba, wata babbar matsala ce ta yin gudan hijira a yankin Afirka ta yamma tare da hadin gwiwar abokan hulda daga kasashen waje a fannin kula da yin hijira ta hanyar amfan da kudadensa da kwarewarsa na sanin tsaron iyaka da kula da harkokin gudun hijira.

Ya kasan babbab kadara ga Nijeriya, Jakadan kula da gudun hijira, mai agaza wa al’umma, mai fafutukar samun zaman lafiya da tsaro, kwararren masani, amintaccen mai kula da kayan aiki da aiki da aka dora masa, wanda ya kafa tushen kula da harkoki shige da fice na zamani a Nijer-iya tare da samun nasarar gina irinsa na farko. Sannan ya gida katafaren sashin fasaha a shalkwatar hukumar shige da fice ta Nijeriya a 2021 a karkashin Shugabacin Muhammad Buha-ri, wani aiki da ke kula da ingantaccen tsaron kan iyakoki da gudun hijira a Nijeriya ta hanyar amfani da fasahar zamani da tsarin iko daga cibiyar bayar umurni da iko ta hukumar shige da fice ta Nijeriya da ke hedkwatar hukumar a Abuja.

Sannan ya wallafa mujalla kan harkokin shige da fice da littattafan da suka kasance kayan aiki ga gwamnati da cibiyoyin masu zaman kansu da al’ummomin kasa da kasa daga a shekarar 2017 zuwa 2021 a kowane wata.

Muhammad Babandede ya kasance dan kishin kasa ne, sannan zai yi iya bakin kokarinsa na yin aiki tukuru idan ya samu damar zama Sanata a yankin arewa maso gabas na Jihar Jigawa.

Shugaban kafar sadarwa ta Hallbibe da ke Abuja, James Sunday, FCAI, MNIIA, wanda ya kasance tsohon mai magana da hawun hukumar shige da fice na Nijeriya ya rubuta hakan.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *