Martani Dangane Da Hayaniyar Ofishin Jakadancin Rasha Kan Mukalar Azu Game Da Putin

[ad_1]

Yayin da nake karanta martanin Jakadancin Rasha ga shafin ra’ayin Azu Ishiekwene a fitowar LEADERSHIP ta ranar 23 ga Janairu, zan aro kalmar da fitaccen Patrick Obahiagbon ya shahara da ita “Igodomigodo” na tsinci kaina cikin rudani mai tsanani.

Martanin Jakadancin Rasha ya bayyana kamar ya kauce daga ainihin makasudin maganar gaba daya.

  • Trump Ya Ce Zai Yi Duk Mai Yiwuwa Don Ganawa Da Putin Da Zelensky Lokaci Guda
  • Xi Da Putin Sun Rattaba Hannu Kan Sanarwar Hadin Gwiwa A Sabon Zamani

Azu, da salon rubutunsa na kawance da koyarwa wanda ya saba da shi, ya yi kokarin sukar da tsawata wa Putin, wanda ya kwatanta da Hitler na zamani, a cikin…

…mutumin Donald Trump, wanda a ganina yake nuna halaye na hadakar sociopath da psychopath.

A kokarinsa na kwatanta Donald Trump da Bladimir Putin wanda tun da fari aka yi ta sukar sa sosai saboda manufofinsa na fadada iko a Crimea da Ukraine Azu ya nuna Putin a cikin haske mafi tsarki fiye da azzalumin da ke zaune a Washington.

Saboda haka, na kasa fahimtar dalilin hayaniyar martani daga Jakadancin Rasha kan wata mukala da ta fi kama da wanke suna da tsarkake Putin fiye da halin hauka na wanda ke zaune a Fadar White House.

Mukalar mai taken “We Owe Putin an Unreserbed Apology” ba roko ba ce duk da karantarta kai tsaye da ake yi a madadin Shugaba Bladimir Putin, kuma ba yunkurin sake jujjuya abin da ake kira “tsare-tsaren ra’ayin Yamma” game da Rasha ko shugabancinta ba ce. Mukalar satire ce: takamaimai, da gangan, kuma mai kaifi, wadda aka nufa kai tsaye ga Shugaban Amurka Donald J. Trump, wanda abubuwan da yake kafa wa gaba suna da hadari…

…kalamansa da ayyukansa na iya sa zalunci ya zama abin al’ada a harkokin duniya.

Duk wanda ya karanta fiye da kanun labarin zai gane hakan nan take. Shafin ra’ayi yana jagorantar masu karatu ta cikin kwatance mai cike da kiyayya da barkwanci, inda mafarkai na fadada ikon Trump daga mamaye Canada zuwa kwace Greenland “Ta kowace hanya,” har zuwa kwaikwayon sauya gwamnati a Benezuela ake amfani da su don nuna faduwar iyaka, hankali, da daidaiton dabi’a a harkokin siyasa na duniya.

A cikin mukalar, Putin bai bayyana a matsayin wanda ake kai hari ba, sai dai a matsayin madubi na magana, wani abu da ake amfani da shi don bayyana muguntar Trump.

Mukalar ba ta goyi bayan ayyukan Rasha a Ukraine ba; a maimakon haka, tana sake bayyana su da sosai: mamayar Crimea, mamayar cikakken yaki, babbar asarar rayuka da ya haifar, da rashin wani dalili mai inganci bisa dokokin kasa da kasa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *