Barkewar Rikici Da Gaba Tsakanin Dangi Bayan Rabuwar Aure
[ad_1]
Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauran su.
Tsokacinmu na yau zai yi duba game da abin da ya shafi barkewar rikicin ma’aurata bayan rabuwa ta shiga tsakani, tare da makomar yaransu.
- Karuwar Mace-mace A Asibitocinmu Sakamakon Sakacin Jami’an Lafiya
- ‘Yan Bindiga: ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Uku Gami Da Kwato Bindigar AK-47 A Gombe
Wasu daga cikin ma’aurata na kokawa game da irin rikicin da ke barkewa tsakanin juna, har ta kan kai ga abin ya zama tamkar yaki tsakanin dangi biyu, kamar ba a taba zaman aure ko surikantaka da juna ba. Sanadiyyar yaran da ke tsakani, kowane daga cikin ma’auratan, na ganin shi yafi dacewa da kulawar tarbiyyar yaran, wanda sanadiyyar hakan rikici ke barkewa.
Dalilin hakan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; “Ko me yake haifar da hakan?, ko akwai wasu matsaloli da hakan ke iya haifarwa?, Yaya makomar yaran ke kasancewa?, Ta wacce hanya za a shawo kan matsalar da ke faruwa ga yaran da suka tsinci kansu a haka?, Wacce shawara ya kamata a bawa ma’autan da hakan ke faruws da su?”.
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Hauwa Abubakar Sarki, daga Jihar Neja:
Abu na farko shi ne su fahimci junan su, idan babu fahimtar juna sai a sanya magabata su shiga lamarin. Domin mutuwar aure ba yaki bane, Allah’n da ya ce ayi aure kuma shi ya ce ayi saki. Wani rabuwa ga ma’auratan shi ne masalaha, musamman idan da cutarwa a tsakani. Idan da zuri’a a tsakani an rabu ne ba a rabu ba. Abin da ke haifar da hakan rashin fahimtar juna daga dukka bangaren. Shawara, su tausashi zuciyarsu, su samu fahimtar juna a tsakanin su. Ba a ce dole su mayar da auren ba domin shi aure rai ne da shi, goben ‘ya’yansu za su duba.
Sunana Aminu Adamu, Malam Madori, A Jihar Jigawa:
To, abin da ke jawo haka rabuwar aure. Hakika hakan yana haifar da matsaloli masu tarin yawa musamman ta fannin tarbiyyar yara, domin tarbiyya aikin mutum biyu ce ma’ana uwa da uba a matakin farko don haka dole za a samu matsala idan iyayen basa tare. Domin daya daga cikin su zai gaza sauke nauyin tarbiyyar da ya rataya a wuyansa. To shawara su iyayen su yi hakuri da junansu koma zaman aurensu, muddin akwai damar hakan domin shi ne zai basu damar gudanar da cikakkiyar tarbiyya.
Sunana Hafsat Sa”eed, daga Jihar Neja:
Uwa dai uwa ce, duk inda uwa za ta, ba za ta taba barin dan ta ya samu matsala ko ya lalace ba, ko da kuwa ita lalatacciyar ce ba za ta so danta ya lalace ba, za ta so dan ta ya samu tarbiyya. Magana ta gaskiya barin da a gidan iyaye ko bangaren uba, yana kawo matsaloli sosai domin ni ya faru a kaina. Wani za a ga matar da ya aura ba ta iya rike ‘ya’yan da ba nata ba, wani kuma ko an bar wa Kaka, ko dangi, yara su yi ta wahala. A bar maka yaro ba boko bare islamiyya wasu ma a kai su kauye. In ka biya kudin makarantar yaro sai a kaishi ta gwamnati ya hadu da abokan banza ya lalace da yawace-yawace da dauke-dauke, in ka nemi a baka danka a hana ka. Ga wata dabi’a da wasu ke ganin idan uwa ta rike yaranta sai a ce ai ‘ya’yan mace ne.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, a Jihar Filato:
Allah dai ya kyauta. Darasin wannan mako abu ne da yake yawan faruwa a tsakanin al’ummar mu, kodayake ba za a ce a wajen mu ne kawai ake samun haka ba. Amma a cikin al’ummar da take tutiya da tarbiyyar addini da riko da koyarwar addinin Musulunci, babban kuskure ne a ce sabani akan makomar yara bayan rabuwar aure ta haifar da mummunar ma’amala da gaba mai tsanani. A bisa koyarwar malaman Musulunci, hakkin uwa da na danginta ne rikon yara bayan rabuwa ko rasuwa. Amma saboda tsoron samun matsala a wajen tarbiyyar rayuwar yaro da dawainiyarsa ta yau da kullum, an fi karfafa ganin miji da danginsa ne suka karbi rikon yara. Sai dai ko ma dai a wanne bangaren rikon yara ya koma, bai kamata a rika samun yawan kai ruwa rana da rashin mutunci a tsakanin dukkan bangarorin biyu ba, wadanda suka kasance surikai a baya.
Sunana Muhammad Isah, Zareku Miga, a Jihar Jigawa:
Na farko ita kanta macen ya kamata tayi hakuri saboda tarbiyyar yaronta, idan a wajenta ne za ka ga tarbiyar tana da wahala, saboda yara basa jin maganar iyayensu mata sosai. Matsaloli akwai su kala-kala, za ka ga yaran basa samun cikakkiyar tarbiyya, kulawa, karatunsu, cinsu da shansu, suturar su idan ba a gaban iyayensu maza suke ba to wannan yana bawa irin wadannan yaran wahala. Shawara a nan iyayensu su yi hakuri idan da damar komawa zaman auren, idan kuma babu to, a bar su a gaban iyayensu maza, saboda wata dawainiyar sai iyaye maza.
Sunana Hadiza Ibrahim D. Auta, Kaura-Namoda, Jihar Zamfara:
A tunanina kowane aure idan aka yi shi tsakanin gefe biyu, ana zama ‘yan’uwa ko da ba a hada jini ba. Amma wani sa’in abin yana juyawa kiyayya da adawa mai girma. Har kullum ana son ko da aure ya rabu a yi duba da yaran da auren ya samar, domin a mutunta su ta hanyar rufa wa juna asiri. Saboda ita tarbiyya a tsakanin uwaye biyu take, ko da tsautsayin rabuwa ya kama ba a rabu ba saboda yaran. Ya kamata a gudu tare a tsira tare. A irin matsalolin da hakan ke haifarwa, wani uban zai iya yin zuciya ya ce ya bar mata yaran idan ta hana shi rike su, ko kuma ita ta yi zuciya ta ce ba za ta sake kula su ba, ta bar shi da su. Uwaye su sauke girman kai su bai wa yaransu kulawa ko da ba a tare.
Sunana Jibrin Yusuf Kaila, daga Hadejia, a Jihar Jigawa:
Rabuwar iyaye, na daya daga cikin abubuwan dake tarwatsa tarbiyyar yara, domin daga lokacin da aka ce yaro iyayensa ba sa tare, shi kenan tarbiyyarsa za ta shiga wani hali, domin wata kulawar ya rabu da ita kenan har abada. Rashin samun wannan kulawar na kai ga yaro shiga hulda da munanan abokai, wanda ba za a gane ba, sai daga karshe za a fahimci illar da hakan ya yi a rayuwarsa, yayin da ba zai yiwu a iya gyarawa ba. Hausawa na cewa, “Tun ran gini, ran zane!” Akwai bukatar iyaye su rika kai zuciya nesa, wajen yin saki. Da wata rabuwar gwara a yi hakuri ko don makomar ‘ya’yan da aka haifa, samun fahimtar ku a tsakani na sanya yara nutsuwa, ko da kuwa kun rabu da juna.
Sunana Rukayya Ibrahim Lawal, daga Jihar Sokoto:
A tunanina wannan mas’alar na samo asali ne daga zafafawa yayin da aka samu rabuwar aure, kowannensu yana ji cewa shi ne akan daidai kuma ya kasa karbar laifinsa. A lokacin ne zuciya take raya musu bari na karbe yaron don na kuntata masa/mata, ita ma ta ji irin yadda na ji. Kuma wannan al’amarin ya kan cutar da walwalar yaransu wani lokacin ma ya taba tarbiyyarsu. Idan da hali iyayen su daidaita junansu, su tarbiyyantar da yaransu a tare, idan ba hali sai a duba yanayin rayuwa ta fuskar tsaro, tsare mutuncin yaro da kula da bukatocinsa. Idan zai fi samun duk wadannan a gun uba to, yana da kyau uwa ta hakura yaro ya zauna a hannunsa, haka ma idan a wajenta zai fi samu.
Sunana Nura Garba, Tsanyawa, Jihar Kano:
A nawa ra’ayin abin da ke haifar da haka shi ne, kaucewa tafarkin addinin muslunci akan aure ko da kuwa saki ya shiga tsakani, domin addini ya tsara komai ko da kuwa akwai son zuciya a ciki. Matsalolin su ne; lalacewar tarbiyyar ‘ya’ya ko da kuwa mace ce ko namiji. Hanyar da za a bi, kowa ya ajiye bacin ran da ya jawo rabuwar auren, a fuskanci sauke nauyin da Allah ya dorawa kowa akan ‘ya’yan. Shawara ita ce tunda farko idan mace ko namiji za su yi aure, su ajiye son rai ko na zuciya wajen fuskantar aure matsayin ibada, ba iya jin dadin duniya ba, domin son zuciya bacin ta.
Sunana Aisha T. Bello, daga Jihar Kaduna:
Mafi yawanci ana rabuwa da juna sai a fara magana kan yara, kuma yaran nan in babu iyayen su mata a gida tarbiyyar su lalacewa take yi gaskiya. Hakan na haifar da matsala, ita tarbiyya na hannun iyaye mata. Ssaboda namiji ba shi da lokacin da zai kula da tarbiyyar yana kasuwa ko ofis. Wasu mazan cewa suke yi in har made ita za ta tafi da yaran to, ciyarwa na wajenta, alhalin hakkin ba nata bane. Dan Allah maza masu irin wannan hali ku ji tsoron Allah, ku bari, ku tuna cewa wannan yara amana ce Allah ya baku.
Sunana Muktari Sabo, Jahun, Jihar Jigawa:
Hakika mutuwar Aure tana haifar da abubuwa da yawa na rashin dadi. Matsala ta farko dake faruwa ita ce matsalar tarbiyya domin yaron da baya tare da iyayensa to, tarbiyyarsa sai a hankali domin yana iya tasowa babu tarbiyya me kyau sakamakon rashin kasancewa da iyayensa. Hanyar da za a bi, na farko iyaye su yi hakuri idan haka ta faru su ci gaba da kulawa da tarbiyyar yaron, ba tare da suna tuna abin da ya faru a tsakaninsu na rashin dadi ba. Domin shi yaron bai da laifi, sannan su tabbatar suna kula da hakkinsa a ko’ina yake.
Sunana Anas Bn Malik Achilafiya, Yankwashi Jihar Jigawa:
Yawanci yana samo asali ne daga rashin fahimta, kuma ma’auratan kan manta cewa duk da sun rabu a zaman aure, alhakin tarbiyya da kula da yaro har yanzu na kowa ne. Abin da hakan ke janyo wa, sabani mai tsanani, har ya mayar da dangi biyu kamar abokan gaba. Matsalolin yara kuwa ciki har da damuwa ta zuciya, rashin kwanciyar hankali, rikicewar tarbiyya, da kuma rasa kulawa ko soyayyar daya daga cikin iyaye.
[ad_2]
Source link