Malamin firamare ya samu kyautar N50m, mota da gida

[ad_1]



Solanke Francis Taiwo, ya zama gwarzon malamin makaranta a Najeriya na shekarar 2025, inda ya lashe kyautar Naira miliyan 50, sabuwar mota, da kuma ƙayataccen gida mai dakuna biyu.

Wasu malamai 11 da suka yi fice, waɗanda aka zaɓa daga cikin jerin sunayen da aka tattara daga jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, suma sun samu kyautar Naira miliyan 25 kowannensu.

Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da tsarin girmama malamai bisa jajircewarsu, ƙirƙira da tasirin da suke yi wajen inganta koyo da koyarwa.

An gabatar da kyaututtukan, waɗanda suka kai jimillar Naira miliyan 325, a taron babban taron malaman Najeriya da aka gudanar a Abuja ranar Talata.

Solanke malami ne a Ansar-ud-Deen Main School da ke Kemta-Ilawo a ƙaramar hukumar Abeokuta ta Kudu a jihar Ogun.

Sauran waɗanda suka samu kyautar sun haɗa da David Kachollom Joseph na GSS Nyango-Gyel, jihar Filato, Malam Musa Abubakar Garba na GSS Tudun Wada, jihar Kaduna, Ifetike Hope Chekwube na GTC Onitsha, Jihar Anambra da Obafemi Peter Lawal na Oriwa Senior Model College, Ikorodu, jihar Legas da Johanna Gilando da Bashar Hantsi na Argungu Emirate Model Primary School, Jihar Kebbi.

Sauran sun haɗa da Blessing Ikong, Chinwe Ituma, Gombo Lawan, Khadijat Galadima da Okide Ochike.

A yayin taron, Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana malamai a matsayin masu gina ƙasa, inda ta jaddada cewa ci gaban ƙasa yana farawa ne da ingantacciyar koyo da koyarwa.

Ta sake tabbatar da kudirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na zuba jari wajen jin daɗin malamai, ci gaban ƙwarewa da samun sabbin basira.

Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ya ce taron ya nuna cewa babu wata ƙasa da za ta iya yin ci gaba fiye da ingancin malamanta, inda ya ƙara da cewa ƙarfafa malamai na cikin manyan manufofin gyaran ilimi a Najeriya.

Shugaban Ƙungiyar Malaman Najeriya (NUT), Ƙwamared Titus Amba, ya gargadi cewa gyaran ilimi zai ci gaba da kasancewa mai rauni muddin ba a magance matsalar albashi da walwalar malamai ba.

Ya ce: “Rashin isasshen kuɗi shi ne babban ƙalubalen da ke lalata ƙwarewar harkar koyarwa.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *