Gwamnatin Turkiyya Na Shirin Zuba Jarin Kasuwanci Na Dala Biliyan 5 A Nijeriya — Shugaba Erdogan

[ad_1]

Shugaban Ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya jaddada ƙudirin ƙasarsa na saka jarin da ya kai dala biliyan 5 a fannin kasuwanci da Nijeriya.

Shugaba Erdogan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Ankara, yayin taron manema labarai na haɗin gwiwa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a yayin ziyarar aiki ta Shugaban Najeriya zuwa Turkiyya.

Erdogan ya ce an soma tattaunawa kan cimma wannan buri, tare da amincewa da kafa Kwamitin Haɗin Gwiwar Tattalin Arziki da Kasuwanci (Joint Economy and Trade Committee) tsakanin ƙasashen biyu, domin faɗaɗa damar kasuwanci da ƙarfafa zuba jarin ‘yan kasuwar Turkiyya a Najeriya.

Ya yaba da jajircewa da ƙudirin Shugaba Tinubu wajen jawo zuba jari, yana mai cewa halartar ministoci da manyan jami’ai daga Nijeriya wata bayyananniyar shaida ta wannan aniya

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *