’Yan bindiga sun sace mata da yara sama da 40 a Zamfara

[ad_1]



’Yan bindiga sun sace mutane sama da mutum sama da 40 a wani hari a yankin Tashar Kuturu da ke kauyen Jangebe da ke Karamar hukumar Talata Mafara ta Jihar Zamfara.

A cewar shugaban ƙungiyar Muryar Talata Mafara, Kwamred Kabiru Jangebe, ’yan bindigar sun shigo kauyen da muggan makamai da misalin ƙarfe 1:00 na dare, inda suka girke manyan bindigogi guda biyu suka rika buɗe wuta kan al’umma.

Kabiru ya ce, maharan sun harbi mutum ɗaya a ƙafafu sannan suka yi awon gaba da fiye da mutane 46, ciki har da mata da yara, sa’annan suka “ƙone ƙafafun mutum ɗaya da harsasai, sannan suka yi garkuwa da mata da yara sama da 46,” in ji shi.

Sun kuma ƙone shaguna da dama, ciki har da manyan kantuna uku na kayan abinci da ƙananan shaguna. “Shaguna kusan tara ne suka ƙone bayan sun kwashe dukiya da magunguna.

“Wannan ya jefa al’umma cikin tashin hankali, inda da dama suka gudu cikin daji. Yanzu haka, mutane 48 ba a san inda suke ba, ciki har da mata masu shayarwa,” in ji Kabiru.

Ya ƙara da cewa, harin ya ɗauki tsawon sa’o’i biyu, inda jami’an tsaro suka kasa tinkarar ’yan ta’addar saboda ƙarfin makaman da suka zo da su. “Sun yi amfani da manyan bindigogi irin waɗanda ake ɗora a kan motoci, hakan ya sa jami’an tsaro suka kasa haye musu,” in ji shi.

Sai dai har yanzu akwai sabani kan adadin mutanen da aka sace. Wani dattijo a kauyen ya shaida cewa, ba a tantance adadin ba tukuna. “Na tattauna da Hakimin yankin, ya ce ba a san adadin ba tukuna. Na umarce su da su yi bincike gida-gida domin tattara sunayen waɗanda suka ɓace,” in ji shi.

Rundunar sojoji daga Anka ta amsa kiran gaggawa da motar sulke, amma ’yan bindigar sun raba hankalin jami’an tsaro ta hanyar hasken fitila da harbi a sassa daban-daban na kauyen.

A cewarsa, sojojin sun yi ƙoƙarin toshe hanyar da ’yan bindigar za su bi a Tunkar Kasara, amma ana zargin wani ya sanar da su, suka canja hanya. Daga baya aka bi sawunsu har zuwa Dangulbi, amma ba a gano mafakar su ba.

Binciken da aka yi daga baya ya nuna cewa, mutane 22 ne aka tabbatar da ɓacewarsu, ciki har da mata masu shayarwa biyar, na miji babba daya, sauran kuma yara ne. Wani yaro ya samu ya tsere.

Haka kuma, ’yan bindigar sun shiga shaguna biyu inda suka kwashe wayoyi, sannan suka kama wasu mutane biyu a gidajensu tare da kwace jakunkunan wayoyin da aka ba su domin caji.

Lokacin da aka tuntubi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Zamfara, DSP Yazid Abubakar, bai amsa kira da saƙon da aka tura masa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *