Tutar APC Ta Fara Kaɗawa A Gidan Gwamnatin Kano Tun Kafin Dawowar Gwamna Abba Jam’iyyar

[ad_1]

A yau Litinin, an daga tutocin jam’iyyar APC a Gidan Gwamnatin Jihar Kano, a matsayin shirin maraba da dawowar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar mai mulki.

Ana sa ran Gwamna Yusuf zai yi rajistar zama mamban APC tare da ƴan Majalisar Dokoki 22, da ƴan Majalisar Wakilai 8, da shugabannin ƙananan hukumomi 44 duk a yau.

  • Ganduje Ya Koma Abuja Daga Landan, APC Na Shirye-shiryen Karɓar Gwamnan Kano
  • APC Ta Musanta Bai Wa Gwamnonin Da Suka Sauya Sheƙa Tikitin Takara Na Kai Tsaye A 2027

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Dawakin-Tofa, ya fitar a ranar Lahadi, an ce dawowar gwamnan APC na bisa la’akari da “halin da ake ciki na shugabanci, da haɗin kan ƙasa da ci gaban jihar.”

Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnan zai yi amfani da wannan damar wajen ƙaddamar da aikin rajistar intanet na mambobin APC a Kano.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *