Yaƙin Amurka Da Iran: Muna Shirin Ƙulla Yarjejeniya – Trump

[ad_1]

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa an yi tattaunawa tsakanin Amurka da Iran, a cikin kwanakin da suka gabata, wanda ya ce ɓangarorin biyu sun cimma manyan matsaya tare da nuna cewa dukkansu na son ƙulla yarjejeniya.

Ya ƙara da cewa wakilinsa na yankin Gabas ta Tsakiya, Steve Witkoff, da surukinsa, Jared Kushner, sun tattauna da Iran a ranar Lahadi, kuma za a ci gaba da tattaunawar a ranar Litinin.

  • Trump Ya Ce Amurka Za Ta Ci Gaba Da Yaƙi Da Iran Ba Tare da Taimakon Kowa Ba
  • Kasar Sin: Kashe Shugabanni Da Hare-Hare Kan Fararen Hula A Iran Abu Ne Da Ba Za A Lamunta Ba

Trump ya ce Amurka na tattaunawa da wani “babban mutum” a cikin gwamnatin Iran, kan batutuwa guda 15 domin kawo ƙarshen yaƙin ciki harda buƙatar Iran ta daina mallakar makaman nukiliya, amma wannan mutumin ba sabon jagoran addini ba ne, wato Mojtaba Khamenei.

Tun da farko, Trump ya ce Amurka da Iran sun tattauna kan daidaita rikici a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ya kuma bayyana cewa zai jinkirta kai hare-haren Amurka kan tashoshin lantarki na Iran na tsawon kwanaki biyar bayan samun “tattaunawa da Tehran.

Sai dai kuma, kamfanin dillancin labarai na Fars, wanda ke da alaƙa da rundunar IRGC ta Iran, ya musanta wannan tattaunawar, yana mai cewa babu wata hulɗa kai tsaye ko a fakaice tsakanin Iran da Amurka.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *