Kuri’un CGTN Sun Nuna Gamsuwar Masu Bayyana Ra’ayi Dangane Da Daidaito Da Tabbacin Ci Gaban Sin Gabanin Taron Boao

[ad_1]

Dandalin Asiya na Boao na bana, wanda zai gudana a yayin da kasar Sin ta fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15, yana matukar jan hankalin sassan kasa da kasa. A gabar da duniya ke fuskantar tarin yanayi na rashin tabbas masu sarkakiya, kasar Sin a nata bangare na nacewa samar da ci gaba, wanda hakan ya sa ake kallonta a matsayin kasa mai tsaro, abar dogaro, kuma wadda ake iya hasashen daidaitonta.

Game da hakan, alkaluman da aka tattara sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, suka nuna yadda kaso 94.9 bisa dari na al’ummun sassan duniya suka gamsu da daidaiton manufofi, da dorewar muhimman fifikon da Sin ke da su ta fuskar ci gaba mai inganci.

Kazalika, kaso 87.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun amince cewa, babbar kasuwar kasar Sin za ta samar da muhimman damammaki ga daukacin kasashen duniya. Har ila yau, kaso 91.2 bisa dari sun bayyana yadda Sin ke fadada bude kofa bisa babban matsayi, a matsayin manuniya ta jajircewa, da karfin gwiwar kasar a fannin ingiza tattalin arzikin duniya.

Daga cimma nasarar kammala shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14, zuwa kyakkyawan mafari na fara aiwatar da shirin karo na 15, sannu a hankali Sin na ci gaba da mayar da mafarkinta zuwa matakan ci gaba na zahiri, ta hanyar tsara ayyuka a matsakaitan matakan da ma na dogon lokaci. Bugu da kari, kuri’un jin ra’ayin jama’ar sun nuna yadda kaso 93 bisa dari suka bayyana gamsuwa ga salon kasar Sin na nacewa wanzar da matakai, da ci gaba na tsawon wa’adi, ta hanyar tsare-tsare bisa matsayin koli, masu samar da kyawawan misalai ga al’ummun kasa da kasa. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *