EFCC Ta Sanya Alama Kan Kadarorin Malami Da Ake Bincika

[ad_1]

Jami’an EFCC sun yi alama kan wasu kadarorin tsohon AGF, Abubakar Malami, a Abuja da Kano. An ce matakin na da nasaba da binciken zargin almundahanar kuɗi da ake yi masa a halin yanzu.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa hukumar ta samu umarnin kotu kafin ɗaukar matakin. An bayyana cewa an yi alamar ne domin sanar da jama’a cewa kadarorin na ƙarƙashin bincike.

  • El-Rufai Zai Amsa Goron Gayyatar EFCC A Ranar Litinin — Lauyansa
  • ’Yansanda Sun Ceto Wani Malamin Addini Da Matasa Suka Tsare A Jihar Gombe

Kadarorin sun haɗa da gidaje, da. otal-otal, da makarantu da masana’antu a wurare daban-daban. Daga ciki akwai Meethaq Hotel, da Harmonia Hotels da kuma cibiyoyin Rayhaan da darajarsu ta kai biliyoyin naira.

Haka kuma rahotanni sun nuna akwai wasu kadarori a Kano da suka haɗa da otal da cibiyoyin kasuwanci. Jimillar darajar dukiyar da aka ambata na nuni da girman binciken da ake gudanarwa.

An ce Malami, wanda aka tsare kan zargin sama da faɗi ya samu beli tare da iyalansa. A wani bidiyo, ya tambayi dalilin yi wa kadarorinsa alama tare da buƙatar ganin umarnin kotu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *