Sin Za Ta Dukufa Wajen Cudanya Da Bangarori Daban Daban Da Batun Yankin Gabas Ta Tsakiya Ya Shafa
[ad_1]
Manzon musamman na gwamnatin kasar Sin mai kula da batun yankin Gabas ta Tsakiya Zhai Jun, ya yi bayani game da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, da abubuwan masu nasaba da ziyarar aiki da ya gudanar ta shiga-tsakani kan batun yankin, yayin taron manema labaru da aka gudanar da yammacin yau Litinin a birnin Beijing.
Zhai Jun ya bayyana cewa, kasashe da jama’a dake yankin Gabas ta Tsakiya, yanzu haka suna begen samun zaman lafiya. Don haka ya kamata bangarori daban daban da abin ya shafa su gaggauta dakatar da daukar matakan soji, da magance tsanantar yanayin da ake ciki a yankin.
Kazalika, a cewar jami’in, kasashen dake yankin suna fama da tasirin yakin, suna kuma nuna damuwa sosai, don haka ya kamata a tabbatar da tsaron rayuwar fararen hulan yankin. Bangarorin sun nuna adawa da rufe mashigin Hormuz, suna kallon kasar Iran a matsayin makwabciya, tare da maraba da yadda Iran din ta taba gabatar da ra’ayinta na daidaita rikicin ta hanyar shawarwari.
Zhai Jun ya yi nuni da cewa, a matsayin kasa mai sauke nauyin dake wuyenta, Sin za ta dukufa wajen cudanya da bangarori daban daban da batun ya shafa, don sassauta rikicin, da sa kaimi ga shimfida zaman lafiya da karko a yankin baki daya. (Zainab Zhang)
[ad_2]
Source link