Najeriya na samun rarar N10bn duk shekara sakamakon cire tallafin man fetur– Sanata
[ad_1]
Sanata Olamilekan Adeola, mai wakiltar Ogun ta Yamma, ya ce Najeriya na samun rarar sama da Naira tiriliyan 10 duk shekara bayan cire tallafin man fetur da kuma aiwatar da sauye-sauyen haraji da Shugaba Bola Tinubu ya kawo.
Ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a Ilaro, a Jihar Ogun.
Sanatan ya ce a baya gwamnati na karɓar bashi mai yawa a kowane wata domin biyan tallafin mai, lamarin da ke jefa tattalin arzikin ƙasa cikin matsala.
“Kafin cire tallafin mai, Najeriya na karɓo bashin biliyoyin Naira a kowane wata, wanda ke kai wa sama da Naira tiriliyan 10 duk shekara,” in ji Adeola.
Sanatan ya ce sauye-sauyen sun taimaka wajen daidaita tattalin arziƙin Najeriya tare da bai wa gwamnati damar yin tsari mai kyau.
Ya kuma ƙara da cewa majalisar dokoki da ɓangaren zartarwa suna aiki tare kan gyaran haraji.
Ya kuma ambaci manyan ayyukan hanyoyi kamar Legas zuwa Kalaba da Sakkwato zuwa babbar hanyar Badagry, inda ya ce ayyukan za su bunƙasar tattalin arziƙi a faɗin ƙasar nan.
“Tallafin mai yana amfanar mutane kaɗan ne, amma cire shi yanzu yana taimaka wa ƙasa wajen adana kuɗi da gina tattalin arziƙin da zai amfanar da kowa,” in ji shi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link