Eid-el-Fitr: Shettima Ya Jaddada Muhimmancin Zaman Lafiya da Ci Gaba a Nijeriya
[ad_1]
A Yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya ke ci gaba da murnar bikin sallah , wani jigo a jam’iyyar APC kuma dan takarar kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Ambasada Yerima Shettima, ya aike da sakon taya murna ga al’ummar Jihar Kaduna, daukacin ‘yan Nijeriya da kuma al’ummar Musulmi baki daya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Kaduna, Ambasada Shettima ya bayyana Eid-el-Fitr a matsayin wani muhimmin lokaci na da ke nuna darussan sadaukarwa, da’a, tausayi da kuma hidima ga adama.
- FIFA Ta Ci Tarar Nijeriya Da Congo
- Mutane 3 Mafi Tasiri A Rayuwar Ƙwallon Ƙafa Ta – Osimhen
Ya ce bai kamata darussan watan Ramadan su kare da azumi ba, sai dai a ci gaba da aiwatar da su a rayuwar yau da kullum ta hanyar kyautatawa juna, hakuri da kuma zaman lafiya tsakanin al’umma.
Shettima , a jaddada bukatar hadin kai ba tare da la’akari da bambancin kabila, addini ko siyasa ba, yana mai cewa ci gaba mai dorewa ba zai tabbata ba sai a cikin yanayi na zaman lafiya da fahimtar juna.
Haka kuma ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan lokaci na bukukuwa wajen karfafa dankon kasa da taimakon juna, musamman ga marasa galihu da masu bukata a cikin al’umma.
Ambasada Shettima ya kuma yaba da kokarin Gwamnan Jihar Kaduna kan jagoranci nagari, ci gaban ababen more rayuwa da kuma kokarin inganta walwalar al’umma.
Ya ce irin wannan jagoranci yana samar da tubali mai karfi ga ci gaba, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da mara baya ga manufofi da shirye-shiryen da ke kawo cigaba da zaman lafiya a jihar.
“Eid-el-Fitr ba kawai lokacin murna ba ne, lokaci ne na tunani da sake jajircewa wajen gina al’umma mai inganci ga kowa da kowa. Mu ci gaba da rike darussan Ramadan a mu’amalolinmu na yau da kullum.”
Ambasada Shettima ya yi addu’ar samun zaman lafiya mai dorewa, ci gaba da hadin kai a Jihar Kaduna da Nijeriya baki daya.
[ad_2]
Source link