Sin Ta Yi Kira Ga Lithuania Ta Nuna Aniyar Gyara Dangantakarsu A Aikace

[ad_1]

Sin ta yi kira ga kasar Lithuania da ta koma kan kyakkyawar turba ta bin ka’idar kasar Sin daya tak a duniya tare da cika sharuddan da za su ba da damar daidaita dangantakar Sin da Lithuania, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin, Lin Jian, ya bayyana a yau Jumma’a.

Lin ya yi wannan jawabi ne a taron manema labarai na yau da kullum lokacin da aka nemi ya yi tsokaci kan bayanan da Firaministar Lithuania, Inga Ruginiene ta yi a baya-bayan nan game da shawarar da kasarta ta yanke a shekarar 2021 ta amincewa a kafa “ofishin wakilcin Taiwan” babban kuskure ne.

Ya ce, kofar Sin ta tattaunawa da Lithuania tana nan a bude. Yana mai cewa, muna fatan Lithuania za ta iya nuna aniyarta ta inganta dangantakar kasashen biyu a aikace, tare da gyara kura-kuranta tun da wuri. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *