EFCC Ta Kama Mutum 11 Masu Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba A Kwara

[ad_1]

Jami’an hukumar shiyyar Ilorin na hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), sun cafke wasu mutum 10 bisa zarginsu da hannu a ayyukan hakar ma’adanai, ba bisa ka’ida ba a Jihar Kwara.

An kama wadanda ake zargin ne a kan babbar hanyar Ilorin zuwa Ogbomosho, sakamakon samun bayanan sirri kan hako ma’adanai, ba bisa ka’ida ba.

  • Rikicin Iran Da Amurka: Gabas Ta Tsakiya Ta Ɗauki Zafi
  • Dabara Ta Rage Ga Mai Shiga Rijiya

Hukumar ta ce, wadanda aka kama sun hada da direbobin manyan motoci tara, da wani dan rakiya.

Wata sanarwa da Dele Oyewale, shugaban sashen yada labarai na EFCC ya fitar, ta ce; an kama wadanda ake zargin ne a yayin wani aiki na “tsattsauran ra’ayi,” tare da tsare su domin ci gaba da bincike.

A cewar hukumar, wadanda ake zargin ba su da sahihin lasisi ko izinin fara ayyukan hako ma’adinai da sufuri.

Har ila yau, an kuma kama manyan motocin da ke jigilar ma’adanan da ake hakowa, ba bisa ka’ida ba a yayin aikin.

Hukumar ta EFCC ta ce, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu, bayan kammala bincike.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *