Gobarar Singa: Abba ya ba da tallafin N100m, ya ba da umarnin gina titin N3bn
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da bayar da Naira miliyan 100 don tallafa wa ’yan kasuwa da suka yi asara sakamakon gobara da ta auku a Kasuwar Singa a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin ziyarar da ya kai kasuwar a ranar Alhamis.
Gwamnan ya nuna alhini kan asarar da ’yan kasuwar suka, inda ya yi alƙawarin taimaka musu.
“Gwamnati ba za ta yi watsi da ku a wannan mawuyacin hali ba,” in ji shi.
Haka kuma, ya ba da umarnin gyara da faɗaɗa hanyoyin kasuwar, sannan ya amince da kashe Naira biliyan uku a kan faɗaɗa tare da inganta manyan tituna, ciki har da Titin Bello, Titin Ado Bayero, Kandoki, Yolawa, da Kwangiri, domin rage ambaliyar ruwa da cunkoson ababen hawa.
Gwamnan ya yi alƙawarin sanya fitilu masu amfani da hasken rana a kasuwar da kuma sabunta kasuwar.
Shuwagabannin kasuwar sun gode wa gwamnan kan tallafin da ya bayar.
Sun yaba wa ƙoƙarin gwamnatin wajen inganta ababen more rayuwa da tallafa wa ’yan kasuwar.