GDPn Kasar Sin Ya Karu Da Kaso 5% A Shekarar 2025

[ad_1]

A wajen wani taron manema labaru da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya a yau Litinin, Kang Yi, darektan hukumar kididdiga ta kasar, ya ce, a shekarar 2025, tattalin arzikin Sin ya kiyaye wani yanayi na samun ci gaba, duk da wasu kalubaloli da ya fuskanta. A cewar jami’in, a shekarar da ta gabata, an dora karin muhimmanci kan bangare mai alaka da sabbin fasahohi, tare da cimma dimbin sakamako wajen samun ci gaba mai inganci. Haka zalika, kasar ta cika manyan burikanta na raya tattalin arziki da kyautata rayuwar al’umma, ta kuma kammala ayyukan da shirinta na raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 ya kunsa, tare da samun sakamako mai gamsarwa. Jami’in ya kara da cewa, bisa kididdigar da aka yi a matakin farko, yawan GDPn kasar Sin a shekarar 2025 ya kai RMB yuan triliyan 140 da biliyan 187 da miliyan 900, adadin da ya karu da kaso 5% bisa na shekarar 2024.

Sauran alkaluman da Mista Kang ya ambata sun nuna karuwar kudin shigar da jama’ar kasar Sin suka samu cikin shekarar 2025, inda saurin karuwar da aka samu a kauyuka ya fi na karuwar kudin shigar mazauna birane. Kana ma’aunin farashin kayayyaki na CPI kusan bai canza ba, idan an kwatanta da jimillar shekarar 2024. Ban da haka, alkaluma sun shaida habakar ayyukan bangaren masana’antu cikin sauri, musamman ma a fannin samar da injuna, da na’urori masu nasaba da fasahohin zamani. (Bello Wang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *