Manyan rikici 5 na iyayen gidan siyasa da yaransu a Jamhuriya ta Hudu
[ad_1]
Tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuraɗiyya a 1999, ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka fi ɗaukar hankali shi ne rikicin da ke tasowa tsakanin manyan ’yan siyasa da yaran gidansu da suka raina a fagen siyasa.
Sau da dama, irin waɗannan rikice-rikice kan rikiɗe zuwa zazzafan faɗa da tashin hankali, lamarin da ke dagula harkokin mulki da tafiyar da gwamnati.
Daga rikicin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo da tsohon Mataimakinsa Atiku Abubakar, zuwa rikicin tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da tsohon Mataimakin, Abdullahi Ganduje, zuwa rikicin Ministan Abuja Nyesom Wike da Gwamnan Jihar Ribas Siminalayi Fubara, siyasar Najeriya ta ci gaba da cika da rikice-rikice tsakanin “uban siyasa” da “yaron gidan siyasa” tsawon shekaru fiye da ashirin.
A daidai lokacin da ake shirin taron Daily Trust Dialogue na 23 mai taken “Jamhuriyar Hudu: Me ke aiki, me kuma ba ya aiki?”, wannan rahoto ya duba manyan rikice-rikice iyayen gidan siyasa da yaransu da suka fi ɗaukar hankali a Jamhuriyar Hudu.
Rikicin Obasanjo da Atiku
Dangantakar Obasanjo da Atiku ta fara ne tun a shekarun 1990, kafin a tsare Obasanjo a gidan yari. Bayan ya fito daga kurkuku, Atiku ta hanyar jam’iyyar PDM ya mara wa Obasanjo baya har ya zama ɗan takarar PDP.
A taron Jos na PDP, Obasanjo ya ɗauki Atiku — wanda a lokacin shi ne zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Adamawa — a matsayin abokin takararsa a 1999. Bayann sun yi nasara tare a 1999, an sake zaɓen su a wa’adi na biyu a 2003.
Sai dai a 2006, rikici ya kunno kai a tsakaninsu. A yayin da ake raɗe-raɗi Obasanjo na son wa’adin uku, Atiku kuma na shirin ya gaje shi.
Atiku ya yi tsayin daka wajen hana hakan tazarcen Obasanjo, har rikici ya yi zafi har ya sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar AC, ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu. Obasanjo ya bayyana kujerar Atiku a matsayin “ta wofi.”
Duk da cewa daga baya rikicin ya lafa, amma ba a samu cikakkiyar sulhu ba. Misali, a zaɓen 2023, duk da ziyarar Atiku ga Obasanjo a Abeokuta, tsohon shugaban bai mara masa baya ba, sai ma ya bayyana goyon bayansa ga Peter Obi na Jam’iyyar Labour.
Rikicin Kwankwaso da Ganduje
Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Ganduje sun yi aiki tare tsawon shekaru, tun daga 1999 zuwa 2003 a matsayin gwamna da mataimaki, sannan daga 2011 zuwa 2015, lokacin da Kwankwaso ya miƙa mulki ga Ganduje.
Amma da Ganduje ya hau mulki, sai ya fara nuna ’yancin kansa, lamarin da ya jawo saɓani tsakaninsu.
Rikicin ya rikiɗe zuwa rikice-rikicen cikin gida a Jam’iyyar APC da kuma tafiyar Kwankwasiyya wadda Kwankwaso ke jagoranta.
A2016, ’yan sanda suka rufe hedikwatar Kwankwasiyya, daga bisani Kwankwaso ya bar APC.
Rikicin ya kara tsananta a zaɓen gwamna na 2019, inda ɗan takarar da Kwankwaso ya tsayar a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar PDP, Abba Kabiru Yusuf, ya sha kaye a hannun Ganduje.
A wa’adin mulkinsa na biyu, Ganduje ya sauke Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, wanda Kwankwaso ya naɗa, ya naɗa Aminu Ado Bayero.
Amma a zaɓen 2023, Abba ya yi nasara a matsayin ɗan takarar Kwankwaso a Jam’iyyar NNPP, kuma ba da jimawa da hawansa mulki ba ya ya dawo da Sanusi a matsayin Sarkin Kano.
Sai da kuma rikicin bai ƙare ba, domin a halin yanzu na rade-radin cewa Gwamna Yusuf na shirin barin NNPP zuwa APC, abin da zai iya jefa Kwankwaso cikin sabon gumurzuda tsoffin “yaransa” biyu a zaɓen 2027.
Rikicin Amaechi da Wike
Ɗaya daga cikin manyan rikice-rikicen siyasa a Jamhuriyar Hudu shi ne na tsoffin gwamnonin Jihar Ribas, Rotimi Amaechi da Nyesom Wike, waɗanda suka fara tafiya a matsayin abokan tafiya tun farkon shekarun 2000, inda suka ƙalubalanci tsohon gwamna Peter Odili a PDP.
Wike ya tsaya kai da fata wajen mara wa Amaechi baya har ya samu nasarar ƙwace kujerarsa ta gwamna a Kotun Ƙoli bayan zaɓen 2007.
A matsayin lada, Amaechi ya naɗa Wike a matsayin Shugaban Ma’aikatan ofishinsa.
Dangantakar su ta ci gaba lafiya har zuwa 2011, inda Wike ya mara masa baya a yakin neman zaɓen tazarce. Bayan nasarar Amaechi, sai ya sake nuna amana ta hanyar tura sunan Wike a matsayin minista.
Sai dai daga baya al’amura sun fara taɓarɓarewa bayan Wike ya zama Ƙaramin Ministan Ilimi, inda ya fara bayyana burinsa na zama gwamna.
A lokacin da guguwar sauyin siyasa ta kunno kai gabanin zaɓen 2015, Amaechi ya sauya sheƙa zuwa APC, yayin da Wike ya tsaya a PDP don neman kujerar gwamna.
Rikicin ya rikide zuwa zafafan kalamai da tashin hankali a zaɓen 2015, inda Wike ya doke Dakuku Peterside — ɗan takarar da Amaechi ya mara wa baya.
A 2019, rikicin ya sake tsananta yayin da Wike ya nemi tazarce. Har yanzu, duk lokacin da suka samu dama, ba sa rasa kalaman sukan juna mutunci.
Wike ya taɓa cewa: “Ni na yi shi gwamna.” Amaechi kuwa a wata hira da Arise TV a 2025 ya mayar da martani da cewa: “Shi yaro ne. Na ɗauke shi aiki. Idan na ga dama zan iya cewa a’a. Na taɓa zama ubangidansa, shi kuwa ƙarƙashina yake.”
Rikicin Wike da Fubara
Bayan dogon rikicinsa da Amaechi, Wike ya sake shiga saɓanin da yarin gidansa na siyasa, wato Gwamna Siminalayi Fubara.
Dangantakarsu ta kasance ta amana haramta kai ga Wike ya zaɓi Fubara — Akanta-Janar a gwamnatinsa — a matsayin magajinsa.
A jawabin rantsuwar Fubara a ranar 29 ga Mayu, 2023, ya nuna girmamawa ga Wike tare da kalaman godiya.
Sai dai shekarar ba ta kare ba dangantakarsu ta yi tsami.
Majalisar jihar ta cika da magoya bayan Wike, abin da ya jawo rikici tsakanin ɓangarorin biyu.
A ranar 29 ga Oktoba, 2023, wasu ’yan majalisa masu goyon bayan Wike suka yi yunƙurin tsige Gwamna Fubara, lamarin da ya rikide zuwa tashin hankali bayan wani ɓangare na majalisar ya kama da wuta.
Shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani, amma sulhun bai daɗe ba, har ta kai ga ayyana dokar ta-baci da dakatar da gwamnan, mataimakinsa da majalisar jihar na tsawon watanni shida bayan hare-haren da rikicin ya haifar a jihar.
Bayan ganawar Wike da Fubara da Shugaba Tinubu a watan Satumba, inda aka dawo da gwamnan da sauran jami’an da aka dakatar, an ɗauka sulhu ya samu.
Amma a watan Disamba, bayan Fubara ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC, sabuwar matsala ta sake kunno kai.
Fubara na shirin neman tazarce, abin da Wike ya ce ya saɓa wa yarjejeniyarsu.
Daga nan ne magoya bayan Wike a majalisa suka sake yunƙurin tsige gwamnan.
Rikicin Oshiomhole da Obaseki
Kamar yadda aka saba gani a siyasar Najeriya, rikicin “uban siyasa” da “ɗan siyasa” ya sake bayyana a Edo, tsakanin Adams Oshiomhole da Godwin Obaseki.
Oshiomhole ya jagoranci Edo daga 2008 zuwa 2016. A wannan lokaci, Obaseki ya kasance shugaban kwamitin tattalin arziki kuma babban jigo a majalisar zartarwa.
Wannan ya sa Oshiomhole ya amince da shi sosai, har ya mara masa baya a matsayin ɗan takarar gwamna a 2016. Obaseki ya yi nasara cikin sauƙi, kuma shekaru biyu na farko sun kasance masu cike da haɗin kai da jituwa tsakaninsu.
A 2019, Obaseki ya fara aiwatar da manufofi masu zaman kansu, abin da ya jawo saɓani tsakaninsa da Oshiomhole – wanda a lokacin shi ne shugaban APC na ƙasa. Obaseki ya nemi tazarce, amma Oshiomhole ya dage cewa dole a sauya shi saboda rashin biyayya.
Rikicin ya tsananta a watan Yuni 2019, lokacin da majalisar jihar ta rantsar da ’yan majalisa 9 daga cikin 24, wani mataki da ake ganin a matsayin ƙoƙarin hana magoya bayan Oshiomhole samun rinjaye.
APC ta ƙi amincewa, kuma lamarin ya kai kotu. Bayan makonni biyu, Obaseki ya kori kwamishinoni 8 da ake ganin magoya bayan Oshiomhole ne.
A watan Yuli 2019, shugabannin ƙananan hukumomi 18 sun jefa kuri’ar rashin amincewa da Oshiomhole, suka dakatar da shi daga jam’iyyar a jihar. Kwamitocin sulhu na APC sun kasa sasanta rikicin. Obaseki ya ce: “Idan ya dawo da nadama da neman afuwa, za mu iya duba yi masa afuwa.”
A Disamba 2019, majalisar jihar ta kori wasu daga cikin ’yan majalisar da aka hana shiga tun farko. A Fabrairu 2020, rikicin ya ƙara tsananta, inda Obaseki ya nemi a kama Oshiomhole bisa zargin hana zaman lafiya da ƙin bin umarnin doka.
A ƙarshe, Obaseki ya samu ƙalubale a cikin APC, inda aka hana shi shiga zaɓen fidda gwani bisa zargin matsalolin takardun karatu.
A sakamakon haka ya sauya sheƙa zuwa PDP, inda ya sake lashe zaben gwamna a 2020, ya doke Osagie Ize-Iyamu — ɗan takarar da Oshiomhole ya mara wa baya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link