Asiri Ya Tonu: Yadda Aka Kashe Uwa da Ƴaƴanta Shida A Kano
[ad_1]
Mazauna unguwar Dorayi Chiranchi a birnin Kano sun bayyana yadda aka aikata mummunan kisan da ya yi sanadiyyar mutuwar wata mata, Fatima Abubakar mai shekara 35, da ƴaƴanta shida. An ce maharan sun kutsa cikin gidansu a Dorayi Gidan Kwari, suka kulle gidan kafin su kashe su, sannan suka yi ƙoƙarin ƙona gawarwakinsu. Mazauna sun ce Fatima ta kira ƴan uwanta tana neman taimako kafin harin, yayin da wayoyinta daga baya aka ce an same su tare da wani ɗan uwanta, Umar Auwalu.
Rundunar ƴansandan Jihar Kano ta ce ta cafke mutane uku, ciki har da Umar Auwalu mai shekara 23, wanda ake zargin shi ne jagoran tawagar kuma ɗan uwan marigayiyar ne.
- Atiku Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Uwa Da Ƴaƴanta Shida A Kano
- ‘Yansanda Sun Kama Mutane 3 Da Ake Zargi Da Kisan Wata Mata Da ‘Ya’yanta 6 A Kano
A cewar mai magana da yawun ƴansanda, Abdullahi Haruna Kiyawa, an kama su ne a wani aikin sirri da aka gudanar tsakanin daren 17 zuwa safiyar 18 ga Janairu, 2026. Abubuwan da aka ƙwato sun haɗa da wani tufafi da ya jiƙe da jini, da wayoyin marigayiyar biyu, da adda, da kulake da kuɗi. Binciken farko ya nuna Umar ya amsa laifin shiga kisan, tare da zargin tawagar tasu na da hannu a wasu hare-hare makamancin wannan a baya.
Mijin Fatima, Bashir, ya ce wannan lamari ya tayar masa da hankali matuƙa kuma ba zai taɓa mantawa da shi ba. Ya bayyana cewa yana kasuwa ne lokacin da aka kira shi aka shaida masa abin da ya faru. “Da na dawo, na tarar an kashe su da adduna da ƙarafuna masu nauyi kamar Keken ɗinki,” in ji shi cikin kuka, yana mai roƙon Allah Ya gafarta wa iyalansa tare da haɗa su a Aljanna.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya yi Allah-wadai da harin, yana mai kiran sa da mummuna kuma abin da ba za a lamunta da shi ba, tare da umartar hukumomin tsaro su kamo duk masu hannu a ciki su gurfanar da su don fuskantar hukunci.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, su ma sun yi tir da lamarin, suna kira da a hanzarta bincike da shari’a domin tabbatar da adalci da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
[ad_2]
Source link