Abin Da Ya Sa NPA Ta Yi Hadaka Da ‘Snake Island Port’ -Dakta Dantsoho

[ad_1]


Shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa NPA ta Kasa Dakta Abubakar Dantsoho, ya bayyana dalilin da ya sa Hukumar ta yi hadin guiwa da Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Snake Island wadda za ta shafe tsawon shekaru 45.

A jawabinsa a wajen rattaba hannun yarjejiniyar Dantsoho ya sanar da cewa, NPA ako da yaushe, a shirye take wajen samun irin wannan dmar, musamman domin a kara fadada harfkar hada-hadar fannin suurin Jiragen Ruwan kasar nan.

“Wannan yarjejiniyar ta nuna a zahiri ta irin burin Gwamnatin Taryya na ganin an samar da damar gudanar da yin gasa a fannin a tsakanin wadanda suke a cikin bangaren a fadin duniya, kamr dai irinsu Nigerdock, da ke son zuba hannun jarinsu a fannn sufurin Jiragen Ruwan kasar nan, “ Inji Dantsoho.

Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Snake Island an kafa ta ne kan hectka guda 85, wadda kuma ta karade shiyyoyu uku.

Majalisar Zartarwa ta kasar nan ce, ke sanya ido tare da kuma tabbatar ganin an wanzar da kula da kayan aikin Tashoshin Jiragen Ruwan da ke a daukacin fadin kasar nan.

Kazalika, ta amince da kulla wannan yarjejeniyar ce a shekarar 2023.

A na sa jawabin a wajen kulla yarjejeniyar Babban Shugaban Tashar ta Snake Island Maher Jarmakani ya bayyana wannan hadakar a tsakanin Gwamnatin Tarayya da da Nigerdock mai matukar mahimmanci.

Ya sanar da cewa, yarjejeniyar ta kai ta akalla dala biliyan daya wacce kuma za ta bayar da damar zuba hannun jari daga ketare na kai tsaye, inda hakan zai kuma kara daga matsayin Nijeriya wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci a duniy.

“Mun bi duk matakan da suka kamata domin mu tabatar da cewa, an bi ka’ida bayan amincewa da Tashar ta Snake Island da Gwamnatin Tarayyata yi, “A cewarsa.

Jarmakani ya ci gaba da cewa, wannan jarjejeniyar za ta kara saita Tashar ta Snake Island wanda kuma tare da yin aiki kafada da kafada da Hukumar NPA da Ma’iakatar Kula da Tattalin Arziki na Teku da sauran masu ruwa da tsaki a fannin za samu nasarar kai wa gaci.

“Muna fatan samar da ci gaba a fannin hada-hadar sufurin Jiragen Ruwa tare da kuma samar da sabon ci gaba, da za a amfana daga fannin bunkasa Tattalin Arziki na Teku,” Inji Jarmakani.

A shekarar 2005, Nigerdock, ya bayar da wata damar gudsanar da aiki na shiyya da kuma taimaka wa, wajen kara daga matakin Hukumar NPA, wanda hakan ya sanya, Fadar Shugaban Kasa, ta amince da kafa Tashar ta Snake Island.

Kazalika, NPA da kuma Hukumar Kwastam sun sahalewa Snake Island gudanar da aiki a shekarar 2017.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *