Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

[ad_1]


Kotun Jihar Kano ta yanke wa mutane huɗu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same su da laifin kashe Rilwanu Ilyasu, wanda aka fi sani da Nanu, wani Makanike da ke da garejin gyaran mota a unguwar Farawa da ke cikin garin Kano. An gurfanar da su ne kan laifin haɗa kai da kisan kai, bisa tanade-tanaden sashi na 97 da na 221(b) na Dokar Penal Code.

Waɗanda aka yanke wa hukuncin su ne Abubakar Sadiq (Alhaji Sallari), da Abdulmajid Jibrin, da Nasiru Sani da kuma Yusuf Sani. Bincike ya nuna cewa sun kai wa mamacin hari da muggan makamai, yayin da wasu biyun da bayyana su da Nura Farin Boss da Ɗan Bayo suka tsere.

A cewar bayanan lauyar gwamnati, Barr. Safiya Yalwati, waɗanda ake tuhumar sun mamaye gidan mamacin da daddare a ranar 13 ga Afrilu, 2016, ɗauke da gatari da wasu makaman, bisa zarginsa da ya tona musu asiri a wurin jami’an NDLEA wanda ya kai ga kama ɗaya daga cikinsu da kuma kwace musu miyagun ƙwayoyi da kuma  ₦27,000.

Shaidu daban-daban bayyana yadda harin yayi sanadin barin mamacin da munanan raunuka har ta kai ga ya rasa ransa, lamarin da ke da nasaba da rikici tsakanin su kan zargin cin amana da harkokin miyagun ƙwayoyi. Mai gabatar da ƙara ta gabatar da shaidu takwas tare da gabatar da wasu kayayyaki a matsayin hujja, ciki har da gatarin da aka yi amfani da shi wajen kai harin.

Bayan nazarin shaidu da takardun kotu, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta bayyana waɗannan mutane huɗu a matsayin masu laifi, sannan ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta bayyana jin daɗinta da wannan hukunci, inda Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Maude Kabir, ta bakin mai taimaka masa a fannin yaɗa labarai, Abubakar Tijjani Ibrahim, ya ce hukuncin ya tabbata ne don tabbatar da adalci kamar yadda doka ta tanada.

[ad_2]

Source link

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *