Sojoji Sun Daƙile Hare-Haren Ƴan Ta’adda, Sun Kwato Makamai A Borno Da Adamawa
Sojojin Rundunar Operation Haɗin Kai (OPHK) sun daƙile wasu hare-haren da ’yan ta’adda suka kai a sassan jihohin Adamawa da Borno, inda suka ƙwato makamai da harsasai, tare da kashe wasu daga cikin maharan a yayin aikin bin sawunsu.
A wata sanarwa da muƙaddashin jami’in yaɗa labarai na OPHK, Laftanar S.A. Atoko, ya fitar a Maiduguri, ya ce da asubahin Juma’a, 16 ga Janairu, 2026, ’yan ta’adda sun yi yunƙurin kai hari kan sansanin sintiri na Sabon Gari a ƙaramar hukumar Madagali ta jihar Adamawa, ƙarƙashin sashi na 4 na OPHK.
- Hukumar ‘Yansanda A Borno Ta Kwato Harsasai 912
- ‘Yan Ta’adda 11 Sun Miƙa Wuya Yayin Da Sojoji Suka Kashe 8 A Borno
Ya ce Sojoji sun hanzarta tunkarar maharan tare da samun ƙarin taimako daga Kunnen da Rundunar Ƙarfin Mai Sauƙiinda suka fatattaki ’yan ta’addan ba tare da asarar rai ko kayan aiki ba. Bayan haka, an binciki yankin don tabbatar da babu na’urorin fashewa (IEDs) ko tarko.
A wani lamari makamancin haka a ranar, ’yan ta’adda sun kai hari mai yawa daga ɓangarori daban-daban kan Tushen Aiki Na Gaba (FOB) Azir a jihar Borno. Sojoji, tare da taimakon rundunar sama ta OPHK, sun yi musu luguden wuta na tsawon fiye da awa guda, lamarin da ya tilasta wa maharan janyewa.
Atoko ya ce harbin rokar RPG na ’yan ta’adda ya shafi wasu motocin ɗaukar sojoji da dakin kula da CCTV, inda wuta ta lalata wani ɓangare. Duk da haka, sojoji sun ci gaba da riƙe yankin.
An kwato makamai da dama daga hannun ’yan ta’addan da suka haɗa da bututun harba bom na 60mm, da bama-bamai, da na’urorin fashewa da aka ƙera a gida, da harsasan bindigogi masu nauyi da ɗaruruwan harsasan 7.62mm NATO.
Sanarwar ta ƙara da cewa jiragen rundunar sama sun bi sawun ’yan ta’addan da suka tsere, inda aka kai musu hare-haren sama a hanyoyin da suka bi, lamarin da ya janyo mutuwar wasu da dama daga cikinsu.
“Atisayen ya nuna jajircewar sojojin OPHK wajen kare rayuka da dukiyoyi, tare da ƙudirin ci gaba da murƙushe duk wata barazana a yankin Arewa maso Gabas,” in ji sanarwar.