Wang Yi Ya Tattauna Da Sakataren Hukumar Tsaro Ta Rasha
[ad_1]
Jiya Lahadi 1 ga wata, mamban ofishin siyasa kuma darektan ofishin harkokin waje na kwamitin kolin JKS Wang Yi ya tattauna da sakataren hukumar tsaro ta tarayyar Rasha Sergei Shoigu a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Yayin tattaunawarsu, Wang Yi ya bayyana cewa, bisa matsayinsu na manyan kasashe a duniya da mambobin dindindin na kwamitin sulhun MDD, ya dace Sin da Rasha su sauke nauyi bisa wuyansu wajen nacewa kan ra’ayin cudanyar bangarori daban daban, da kiyaye tsarin kasa da kasa karkashin jagorancin MDD, da goyon bayan ra’ayin rarraba iko tsakanin kasashen duniya mai daidaito, da dunkulewar tattalin arzikin duniya mai hakuri da bambancin ra’ayi da amfanar da juna, tare kuma da ingiza kafuwar tsarin tafiyar da harkokin kasashen duniya mai adalci.
Wang Yi ya kara da cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da Rasha domin tabbatar da matsaya guda da shugabannin kasashen biyu suka cimma, ta yadda za su samu sabon ci gaba yayin raya huldarsu a sabuwar shekara ta 2026.
A nasa bangare, Shoigu ya yi tsokaci cewa, kasar Rasha tana fatan za ta ci gaba da gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninta da kasar Sin, tare kuma da bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a matsayin koli, da sa kaimi kan gina duniya mai rarraba iko bisa adalci kuma lami lafiya. (Mai fassara: Jamila)
[ad_2]
Source link